Rabon gado: Iyalin Marigayi Kure za su raba gardama a babban kotun shari’a

Rabon gado: Iyalin Marigayi Kure za su raba gardama a babban kotun shari’a

- Batun rabon gadon wasu gidaje da Abdulkadir Kure ya bari ya sa an tafi kotu

- Yaron marigayin yana karar Mahaifiyarsa da ‘yanuwansa uku a kotun shari’a

- Umar Abdulkadir Kure ya kai kara ne bayan lokacin daukaka shari’a ya wuce

Umar, daya daga cikin ‘ya ‘yan marigayi Abdulkadir Kure, wanda ya yi gwamna a jihar Neja, ya kai kara a kotu a game da yadda aka raba gadonsu.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 3 ga watan Fubrairu, 2021 cewa Umar Abdulkadir Kure ya shigar da karar mahaifiyarsa, Sanata Zainab Kure.

Rahotanni sun bayyana cewa Umar Abdulkadir Kure ya na kalubalantar yadda babban kotun shari’a ta raba wasu gidaje da mahaifin na su ya mutu, ya bari.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

A kara mai lamba SCA/NS/CV/O4/2020, ‘dan marigayin ya nuna bai yarda da kason da Alkali ya yi wajen rabon dukiyar mahaifinsu, tsohon gwamna ba.

KU KARANTA: Buhari ya yi ta'aziyyar tsohon Gwamna Kure

Wadanda wannan Bawan Allah ya yi kara a shari’a mai lamba ta USC/MK/CV/139, sun hada mahaifiyarsa, da sauran ‘yanuwansa uku da aka bar wa gado.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai karar ya roki Alkalin kotun daukaka kara na shari’a ya kara masa lokaci ya shigar da korafinsa, duk da cewa lokacin daukaka shari'a ya wuce tuni.

Mista Umar Kure ya rubuta takarda mai tsawon sakin-layi 16 da shaidar wata mai suna Blessing Abraham, ta na karfafa cewa sai daga baya ya san da rabon.

Blessing Abraham ta bayyana cewa wanda ya kai karar da lauyansa ba su nan a lokacin da aka yi rabon gidajen marigayin a ranar 11 ga watan Disamba, 2019.

Kara karanta wannan

Shugabar Hukumar NIDCOM Ta Cire Rigar Mutunci, Ta Dirkawa Wani Zagi a Twitter

KU KARANTA: 'Diyar tsohon Gwamnan Neja, Kure, ta rasu

Rabon gado: Iyalin Marigayi Kure za su raba gardama a babban kotun shari’a
Sanata Zainab Abdulkadir Kure Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Abraham ta shaida wa kotu sai daga baya ne yaron tsohon gwamnan ya samu labarin matakin da aka dauka, bayan lokacin daukaka kara a kotun ya wuce.

Umar ya ce ba ayi masa adalci a rabon ba, kuma an raba dukiyar mahaifinsu kafin a biya masa bashi.

A lokacin da tsohon gwamnan ya rasu, tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci garin Minna, babban birnin jihar Neja ya yi gaisuwa.

Goodluck Ebele Jonathan da tawagarsa, sun yi ta’aziya ga iyalan marigayi tsohon gwamnan da daukacin mutanen Jihar a game da wannan rashi da kasa ta yi.

Tsohon shugaban kasa ya bayyana wannan a shafinsa ta Facebook a inda yake bayyana tsohon gwamna a masayin jarumi, jigon dan siyasa da ya kawo cigaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Atiku Ya Shilla Turai Ana Tsaka da Gangamin Yakin Neman Zabe

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel