Shugaban kasa Buhari yayi makokin Kure, tsohon gwamnan jihar Niger
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi Magana a kan mutuwar tsohon gwamnan jihar Niger, Abdulkadir Kure
- Shugaban kasar ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da mutanen jihar Niger
- Shugaban kasa Buhari ya kuma jinjina ma kure bisa ga sadaukarwar da yayi don ci gaban jiharsa, da muhimman ayyuka da ya ci gaba da ba garinsa ko bayan da ya bar mulki
A ranar Litinin, 9 ga watan Janairu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bakin cikin sa a kan mutuwar tsohon gwamnan jihar Niger, Abdulkadir Kure.
Shugaban kasar a wata jawabi daga Femi Adesina, mai basa shawara na musammman a kafofin zumunta, ya mika ta’aziyyarsa ga gwamnati da mutanen jihar Niger bisa ga mutuwar tsohon gwamnan jihar, Abdulkadir Kure.
KU KARANTA KUMA: Hajjin 2017: Kasar Saudiya ta shimfida sabon tsari don kare maniyyata
Shugaban kasa Buhari ya kuma nuna tausayawa ga matar marigayin, Sanata Zaynab Kure da ya’yanta, da dukkan yan uwan Kure da mutanen kabilar Nupawa, kan mutuwar.
Karanta cikakken jawabin a kasa:
“Shugaban kasar ya bi sahun su gurin makokin mutuwar nagartacen gwamna kuma gawutacen shugaban siyasa wanda ya kasance mutun mai wanzar da zaman lafiya, ci gaba da kuma hadin kan jihohin Najeriya iya rayuwarsa.
“Shugaban kasa Buhari ya jinjina ma sadaukarwan Engr. Kure gurin ci gaban jihar sa, ya yi kokari da al’umman garinsa ko bayan da ya bar kujerar mulki.
“Shugaban kasar yayi addu’a cewa Allah ya karbi bakoncin ruhin Gwamna Kure ya kuma ba masu makokinsa dangana da juriya.”
Kure ya rasu a kasar Jamus inda yaje ganin likita an tafi dashi kasar waje a makon da ya gabata sakamakon wani rashin lafiya.
Marigayin ya yi gwamnan jihar sau biyu daga shekarar 1999 zuwa 2007.
https://www.facebook.com/naijcomhausa/
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng