Mutuwa riga: Diyar tsohon gwamnan jahar Neja ta rigamu gidan gaskiya
Gwamnan jahar Neja, Abubakar Sani Bello inkiya Abu Lolo ya jajanta ma iyalan tsohon gwamnan jahar, marigayi Abdulkadir Kure, tare da bayyana alhininsa bisa rasuwar guda daga cikin yayan marigayin, Malam Fatima Kure.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Gwamna Abubakar Sani Bello ya bayyana alhinin nasa ne ta bakin kaakakinsa, Malam Jibrin Ndace, inda yake taya iyalan Kure jimamin mutuwar yar uwarsu Fatima wanda ta rasu a ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Kuyi koyi da Buhari – Nuhu Ribadu yayi kira ga sabbin gwamnoni
Gwamnan yayi addu’ar Allah Ya jikan Fatima, kuma Ya sanyata cikin Aljannar Firdausi, sa’annan yayi addu’ar Allah Ya baiwa kafatanin danginta hakurin rashinta, Amin.
Daga karshe sanarwar ta karkare da cewa Gwamna Abubakar ya aika da tawagar wakilansa da suka wakilceshi a wajen jana’izar Fatima da aka gudanar a babban Masallacin Najeriya dake babban birnin trayya Abuja.
Ita dai Fatima Yasmin Kure ta rasu ne sakamakon wani gajeren rashin lafiya da tayi fama dashi, da fatan Allah Ya gafarta mata kurakuranta.
Idan za’a tuna, shima mahaifin Fatima, marigayi Abdulkadir Kure ya taba zama gwamnan jahar Neja daga shekarar 1999 zuwa 2007, inda daga bisani matarsa Hajiya Zainab Kure ta zama Sanata a jahar Neja, a ranar 8 ga watan Janairun 2017 Allah Yayi ma Abdulkadir Kure rasuwa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng