Ta'aziyyar Jonathan ga iyalan marigayi Kure (HOTUNA)

Ta'aziyyar Jonathan ga iyalan marigayi Kure (HOTUNA)

- Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci garin Minna babban birnin jihar Niger da kuma yin ta’aziya ga iyalan marigayi tsohon gwamna jihar Niger.

Ta'aziyyar Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da sarkin Minna, Umar Farouq Bahago

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a ranar Alhamis 12 ga watan Janairu ya kai ta’aziyya ban girma ga iyalan marigayi tsoho gwamna jihar Niger injiniya Abdulkadir Kure wanda Allah ya wa cikawa a kasar Jamus a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu, 2017.

Jonathan kuma ya ziyarci mai martaba sarkin Minna, Umar Farouq Bahago a babban birnin jihar Niger.

Ta'aziyyar Jonathan
Jonathan da iyalan marigayi Kure

Tsohon shugaban kasa ya bayyanar da wannan labari ne a shafinsa ta Facebook a inda yake bayyana tsohon gwamna a masayin jarumi, jigon dan siyasa da kuma taimakawa wajen cingaban kasa

Ya ce “ Godiya ta tabatta ga Allah wanda ya bani damar ziyara garin Minna babban birnin jihar Niger a wannan lokaci da kuma yin ta’aziya ga iyalan marigayi tsohon gwamna jihar Niger injiniya Abdulkadir Kure da mai martaba sarkin Minna, Umar Farouq Bahago.

Ta'aziyyar Jonathan
Jonathan da matan marigayi Kure

Allah ya ba iyalan marigayin juriyar wannan rashi da kuma Allah ya sa al-janat firidaus ne makomar sa.

An kai marigayin ne kasan waje makon da ya gabata bayan wani rashin lafiya, amma Allah ya masa cikawa wasu kwanuka daga baya.

Ta'aziyyar Jonathan
Ta'aziyyar tsohon shugaba Jonathan

Tsohon gwamna ya yi wa’adi biyu a karagan mulkin jihar Niger daga shekara 1999 har zuwa 2007.

Kuma shine gwamnan ta 12 a jerin tsofofin gwamnonin jihar Niger, kuma yana ta 3 a cikin tsofofin zabebben gwamnonin farar hula bayan mai martaba sarki Awwal Ibrahim daga shekara (1979 – 1983) da dokta Musa Inuwa daga shekara (1992 – 1993).

Allah ya jikansa da rahma. Amin.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel