Fatattakar Fulani na daura Najeriya kan turbar hatsari, gargadin dattawan arewa

Fatattakar Fulani na daura Najeriya kan turbar hatsari, gargadin dattawan arewa

- Kungiyar Dattawan Arewa sun nuna rashin jin dadinsu ga fatattakar Fulani a kudanci

- Sun bayyana hakan a matsayin wani yunkurin sanya Najeriya kan turbar hatsari

- Sun kuma bayyana cewa Fulani da dama masu bin doka da oda ne tare da neman na kansu

Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi gargadi kan kuntatawa Fulani masu bin doka da oda a yankin kudancin kasar nan.

Kungiyar a ranar Talata ta nuna damuwarta kan sanarwar korar da aka ba wa Fulani makiyaya, lura da cewa yanayin yana sanya kasar kan turba mai hadari, The Cable ta ruwaito.

Sunday Adeyemo, wani shugaban matasa wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ba da wa'adi ga Fulani makiyaya a karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo.

Bayan bada umarnin, ya ziyarci jihar Ogun ranar Litinin, yana mai shan alwashin “fatattakar” makiyayan da ke kashe mutane.

KU KARANTA: Zan bar aiki cikin farin ciki domin na cika burina, tsohon hafsin sojin sama

Fatattakar Fulani na daura Najeriya kan turbar hatsari, gargadin dattawan arewa
Fatattakar Fulani na daura Najeriya kan turbar hatsari, gargadin dattawan arewa Hoto: The Will News Media
Asali: Twitter

Dangane da lamarin, dattawan arewa sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da sauran jami'an tsaro da su shiga lamarin.

"Kungiyar na karbar rahotannin hare-hare kan al'ummomin Fulani a kudu, tun daga daren Lahadi, 31 ga Janairu,

"kuma mun dauki matakin da ya dace ta hanyar jawo hankalin mahukunta game da hatsarin da wadannan hare-hare ke jawowa ga dukkan 'yan Najeriya," in ji Hakeem Baba-Ahmed, daraktan yada labarai na NEF, ya ce a cikin wata sanarwa.

“NEF ta damu matuka da rahotannin zubar da jini da hare-hare kan Fulani makiyaya a al’ummomin wasu jihohin Kudu.

“Kungiyar ta bukaci a hanzarta a kamo tare da gurfanar da wadanda ke kai wa Fulani hari tare da sanya kasar kan turba mai matukar hatsari.

“Kamar kowane dan Nijeriya da za a iya samun sa a kowane inci na Nijeriya, ba za a tauye‘ yancin Fulanin ba ta hanyar masu aikata laifi da ke fakewa da bukatun kabilanci don wargaza su.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace mahaifin shugaban wata karamar hukuma a Abuja

A wani labarin, Gwamnatin Ogun a ranar Litinin ta karyata rahotannin da ke nuna cewa ta nemi taimakon Sunday Adeyemo, da aka fi sani da Sunday Igboho, don magance laifuka a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar, Abdulwaheed Odusile, ya yi watsi da rahoton a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta sa’o’i bayan Igboho ya isa jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.