Festus Keyamo: Gwamnatin Tarayya ba ta yi karin kudin wutar lantarki ba

Festus Keyamo: Gwamnatin Tarayya ba ta yi karin kudin wutar lantarki ba

-Festus Keyamo ya yi magana game da rahotannin karin kudin wuta

-Karamin Ministan tarayyar yace abin da aka yi ba karin farashi bane

-Keyamo ya kira taro, yace ba a tuntube su kafin a dauki matakin ba

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Festus Keyamo, ya ce gwamnatin tarayya ba ta yi kari a kan kudin shan wutar lantarki ba.

Festus Keyamo ya bayyana cewa an yi wa wasu ‘yan kwaskwarima ne kurum a kan kudin shan wutan, amma abin bai kai ga karin farashi ba.

Ministan ya yi wannan karin haske ne a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin na Channels TV a ranar Talata, 5 ga watan Junairu, 2020.

A cewar Festus Keyamo SAN, hukumar NERC mai kula da farashin wuta ba ta tuntube shi ko ‘yan kwamitinsa kafin daukar wannan mataki ba.

KU KARANTA: Za a kara kudin wuta daga Afrilu

Da aka tambayi Keyamo ko kamfanonin raba wuta za su iya kara farashi, sai ya bayyana cewa sai an zauna da masu ruwa da tsaki kafin a kai ga haka.

Ya ce: “Babu karin kudin da aka yi, abin da mu ka yarda da shi, shi ne, za a taba wasu rukunin masu shan wuta. Kun san mu na da sahu; A, B, C, D.”

“Abin da aka yi shi ne an yi wa wasu rukunin masu shan wutan garambawul, amma ba a kara kudi ba.”

“Mun yi maza mun kira taro a kan maganar, kuma abin da NERC ta fitar ya sha ban-bam da yarjejeniyar da mu ka dauka a kwamiti.” Inji Ministan.

KU KARANTA: An kirkiro manhajar yin katin 'dan kasa

Festus Keyamo: Gwamnatin Tarayya ba ta yin karin kudin wutar lantarki ba
Festus Keyamo SAN a taro Hoto: Twitter Daga: twitter.com/fkeyamo
Asali: Twitter

Ita ma hukumar ta NERC ta fitar da jawabi a jiyan, ta ce rahotannin da ke yawo na cewa an yi karin 50% a kan kudin lantarki, ba gaskiya ba ne.

A sanarwar da NERC ta fitar, ta ce ta canza farashin da ake saida kowane karfin Watt na wuta daga N2 zuwa N4 saboda yadda kaya suka yi tsada.

Wani dalili da hukumar ta bada shi ne an samu tashin dala daga watan Nuwamba zuwa Disamba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar adawa ta PDP ta yi wuf ta yi magana, ta kira matakin da aka dauka da rashin tausayi da imani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel