Dawowar COVID-19: Gwamnati ta fara maganar sake rufe makarantu a Najeriya

Dawowar COVID-19: Gwamnati ta fara maganar sake rufe makarantu a Najeriya

- PTF ta na lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar COVID-19

- Wani jam’in PTF ya bayyana cewa za a iya rufe makarantu idan aka yi wasa

- Kwamitin ya ce idan cutar ta rika yawo, za a kai ga sake garkame makarantu

Kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19 ya bayyana cewa ba zai ki bada shawarar a rufe makarantun kasar nan ba.

Jaridar Punch ta rahoto daya daga cikin ‘ya ‘yan kwamitin shugaban kasar na PTF ya na wannan bayani ne a ranar Litinin, 1 ga watan Junairu, 2021.

Mukhtar Muhammed, wanda ya na cikin manyan wannan kwamiti na PTF ya bayyana cewa ba za su ki cewa ka da ra rufe gari idan abin ya faskara ba.

Kamar yadda rahoto ya zo mana, an ji Malam Mukhtar Muhammed ya na wannan jawabi a wani bidiyo da kwamitin ya wallafa a dandalin Twitter.

KU KARANTA: Yan Sanda za su fara cafke masu saba dokar COVID-19

Ya ce: "Bude makaranta magana ce da PTF ta tattauna da kyau a kanta. Kamar yadda mu ka fahimta, ma’aikatar ilmi ce ta zabi a bude makarantun nan.”

“Yanzu PTF ta na sa ido da lura a kan abubuwan da ke faruwa, idan mu ka ga masu dauke da cutar su na kara yawa, ana samun masu ciwon a makarantu, dole mu tabbatar an rufe makarantun.”

“Tun da farko ya kamata ace an dakatar da bude makarantu, amma tun da an riga an bude su, to PTF za ta cigaba da sa ido sosai a kan duka makarantun."

A cewar Mukhtar Muhammed, PTF za ta dage wajen ganin al’umma su na bin dokoki da sharudan da aka gindaya domin yaki da annobar cutar Coronavirus.

KU KARANTA: Lai Mohammed da Garba Shehu su na bata sunan Buhari – CNPP

Dawowar COVID-19: Gwamnati ta fara maganar sake rufe makarantu a Najeriya
Shugaban PTF Boss Mustapha ya na jawabi Hoto: Twitter
Source: Twitter

Shugaban PTF, Boss Mustapha ya alakanta karuwar masu dauke da cutar da ake samu da bude makarantu da aka yi, inda aka bada damar a koma daukar karatu.

Ministan kwadago na kasa, Chris Ngige ya bada sanarwar cewa zai sa labule da ma’aikatan jami’an da ke barazanar zuwa yajin-aiki saboda rabon kudin alawus.

Gwamnatin tarayya za ta hana wannan yajin-aiki a lokacin da ASUU ba ta dade da dawo ba

Kungiyoyin na Senior Staff Association of Nigerian Universities (SSANU) da Non-Academic Staff Union (NASU) su na yunkurin tafiya yajin-aiki a ranar Juma'ar nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel