Kungiyar CNPP ta yi kira a tsige Ministan labarai Lai Mohammed, da Garba Shehu

Kungiyar CNPP ta yi kira a tsige Ministan labarai Lai Mohammed, da Garba Shehu

- CNPP ta nemi a tsige Ministan yada labarai, Lai Mohammed daga kan kujerarsa

- Kungiyar ta kuma nemi a sallami mai ba shugaban kasar shawara, Garba Shehu

- A cewar jam’iyyun siyasar, wadannan jami’ai su na batawa gwamnatin APC suna

Kungiyar CNPP ta hadakar jam’iyyun siyasar Najeriya ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

CNPP ta na so a tsige Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Alhaji Lai Mohammed da mai ba shugaban kasa shawara kan harkar yada labarai, Garba Shehu.

Malam Garba Shehu shi ne mai magana da yawun bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan kungiya ta na zargin hadimin shugaban kasa Garba Shehu da jawo wa Najeriya abin kunya a gaban idon Duniya da kuma yaudarar al’ummar kasar.

KU KARANTA: An gano al’umma na wasa da dokar rufe fuska inji Hadimin Buhari

Jawabin da CNPP ta fitar ya fito ne ta bakin Cif Willy Ezugwu, inda ya ce Lai Mohammed da Garba Shehu sun zama ala-ka-kai ga gwamnatin shugaba Buhari.

Willy Ezugwu yake cewa sai an fi ganin gwamnatin Buhari da mutunci da ace babu Ministan da hadimin na sa, saboda irin tafka da warwar da su ke ta yi.

Ya ce: “Ministan yada labarai, Mohammed da mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Shehu, ala-ka-kai ne da su ka bata sunan gwamnatin APC mai mulki.”

“A wajen mafi yawan ‘yan Najeriya, an fi sanin Ministan labarai, da yaudarar mutane, kamar hadimin shugaban kasa, sun sa an koma shakkar gwamnati.”

KU KARANTA: Ban bar wa Gwamnati kudi na da aka karba ba – Yari

Kungiyar CNPP ta yi kira a tsige Ministan labarai Lai Mohammed, da Garba Shehu
Shugaban kasa da Garba Shehu Hoto: Garba Shehu
Source: Facebook

“Misali, yaushe ne Ministan yada labarai ya gano cewa binciken rashin gaskiya na CPI da kungiyar Transparency International (TI) ta yi ya zama bai da tabbas.”

Kungiyar ta kuma soki maganar da hadimin Buhari ya yi na cewa an ci karfin Boko Haram.

Dazu kun ji cewa Shugaban Majalisar Borno, Rt. Hon. Abdulkareem Lawan, ya ce karya ce ace babu karamar hukuma da ta ke hannun 'yan ta'addan Boko Haram.

Gwamnati ta na ikirarin babu wani gari da ke hannun Boko Haram, amma shugaban majalisar ya ce shekaru uku kenan babu mutum a kauyen da ya fito na Guzamala.

Abdulkareem Lawan ya ce maganar cewa sojoji sun karbe duka garurwan ‘Yan ta’adda, karya ce.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel