NANS ta gargadi Igboho: Kada ka janyo fitina a Kudu maso yamma

NANS ta gargadi Igboho: Kada ka janyo fitina a Kudu maso yamma

- Shugaban kungiyar dalliban Nigeria reshen jihar Ogun, Kehinde Damilola Simeon, ya gargadi Sunday Igboho kan korar makiyaya

- Shugaban daliban ya shawarci Igboho ya hada gwiwa da hukumomin da abin ya shafa a tattauna domin kare afkuwar rikici a yankin

- Ya yi gargadin cewa hanyar da Igboho ya dako a yanzu idan ba a zauna an yi nazari ba za ta iya haifar da yakin kabilanci

Kungiyar Dalliban Nigeria ta Kasa, NANS, a ranar Talata ta gargadi mai rakkin kare Yarbawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho ya sauya salonsa ya zauna ya tattauna da masu ruwa da tsaki a kudu maso yamma domin gano yadda za a magance matsalar makiyaya a kasar Yarbawa.

Daliban sun ce hakan na da muhimmanci domin kada "ya hura wata fitinar da za ta janyo rushewar doka da oda a yankin," kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

NANS ta gargadi Igboho: Kada ka janyo fitina a Kudu maso yamma
NANS ta gargadi Igboho: Kada ka janyo fitina a Kudu maso yamma. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

DUBA WANNAN: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

Igboho, a ranar Litinin, ya tafi garuruwan Yarabawa a kasar Yewa da ke jihar Ogun domin cigaba da yakinsa na korar makiyaya masu kai hare-hare a kasar Yarbawa.

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi a ranar Talata, shugaban NANS/JCC reshen jihar Ogun, Kehinde Damilola Simeon ya bukaci shi da ya hada gwiwa da hukumomin da abin ya rataya a kansu domin kare afkuwar fitina.

Simeon ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar ta duba yiwuwar yi wa makiyaya da ke iyakokin jihar rajista, ta haramta kiwo a filaye barkatai sannan ta kadamar da rundunar Amotekun don cigaba da yaki da miyagu a harabar makarantu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun harbi tsohon Dan Majalisar Sokoto, sun sace matarsa

"Mun fahimci Igboho, amma muna ganin yana da kyau ya gana da shugabannin Yarbawa, Afenefere da sauran masu ruwa da tsaki.

"Hakan na da muhimmanci domin ba mu son fitina ta barke a Kudu maso yamma saboda rushewar doka.

"Muna ganin abinda Igboho ya ke yi idan ba a yi nazari sosai ba zai iya haifar da yakin kabilanci.

"Don haka muna kira gareshi ya hada gwiwa da hukumomin da suka dace don kiyaye afkuwar fitina," in ji shi.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel