Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona

Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona

- Kotun tafi da gidanka karkashin alkalancin mai shari'a Idayat ta bada umarnin rufe kasuwar Wuse a Abuja

- Kwamitin yaki da yaduwar annobar korona ta kai ziyarar ba-zata kasuwar a ranar Litinin inda ta ga abubuwan mamaki

- Kwamitin ya ce 'yan kasuwar basu amfani da takunkumin fuska, gwada dumin jiki da kuma wanke hannuwa

Wata kotun tafi da gidanka a Abuja ta bada umarnin rufe kasuwar Wuse da ke Zone 5 saboda take dokokin dakile yaduwar cutar korona a kasuwar, The Cable ta wallafa hakan.

An rufe kasuwar UTC da rukunin shagunan Murg da ke yanki na 10 a Garki duk bayan umarnin kotun.

Kwamitin tabbatar da bin dokar korona ta Abuja wacce ta ziyarci kasuwar a ranar Litinin ta bayyana yadda ta samu babu na'urar gwada dumin jiki, ba a amfani da takunkumin fuska da kuma abubuwan wanke hannu a kasuwar.

KU KARANTA: Hotunan karen wata 6 da za a siyar N1.1m ya janyo cece-kuce a kafar sada zumunta

Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona
Kotun Abuja ta bada umarnin garkame kasuwar Wuse saboda take dokar korona. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Kwamitin ya damke wasu mutane a cikin kasuwar a motocin haya wadanda suka ki saka takunkumin fuska. An gurfanar da sama da mutum 100.

Idayat Akanni, alkalin kotun ta yanke wa mutanen hukuncin biyan dubu bibbiyu ko kuma su yi wa yankinsu aikin makonni bibbiyu.

Alkalin ta ce an bai wa masu laifin wannan hukuncin ne saboda wannan ne karo na farko da aka taba kama su da wannan laifin.

KU KARANTA: Da duminsa: APC ta yi sasanci tsakanin Yari da Marafa a jihar Zamfara (Hotuna)

A wani labari na daban, wani mai yakin kwatar 'yancin Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya isa jihar Ogun yana cewa ya kai ziyarar ne don ya fatattaki makiyaya.

Dama Igboho ya bayyana a labarai yana bai wa makiyayan da suke wuraren Ibarapa dake jihar Oyo wa'adin kwanakin da za su kwashe ya nasu ya nasu su bar garin. Bayan nan ne aka kai wa gidan sarkin fulanin yankin farmaki.

Premium Times ta samu bidiyon tattaunawar da aka yi dashi inda yake cewa ya je ne don nema wa 'yan uwansa hakkinsu sakamakon yadda Fulani suke ta kashe su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel