Shekaru 3 kenan kauyenmu, Guzamala ya na hannun Boko Haram inji Rt. Hon. Lawan

Shekaru 3 kenan kauyenmu, Guzamala ya na hannun Boko Haram inji Rt. Hon. Lawan

- Gwamnatin Tarayya ta na ikirarin babu wani gari da ke hannun Boko Haram

- Shugaban Majalisar Borno ya ce shekaru uku kenan babu mutum a Guzamala

- Abdulkareem Lawan ya ce in ban da Yan ta’adda, ba kowa a karamar hukumar

Shugaban majalisar dokokin Borno, Abdulkareem Lawan, ya musanya maganar cewa Boko Haram ba su rike da wata karamar hukuma a jihar Borno.

Premium Times ta rahoto Rt. Hon. Abdulkareem Lawan, ya na raddi ga wasu kalamai da su ka fito daga bakin tsohon hafsun tsaro, Janar Gabriel Olonisakin.

A wajen yi wa tsofaffin shugabannin sojojin kasar bikin ban-kwana, Janar Gabriel Olonisakin, ya yi ikirarin babu yankin da ke hannun ‘yan ta’adda a yau.

Abdulkareem Lawan ya ce ko kadan ba haka abin ya ke ba, Lawan ya ce idan aka fadi haka, to ba ayi wa mutanen Borno, musamman na mazabarsa adalci ba.

KU KARANTA: Inda su Buratai su ka samu matsala - Gwamna Wike

Lawan yake cewa duk da ya na shugaban majalisar dokoki, shekaru uku kenan bai isa ya kai ziyara zuwa kauyensu ba, saboda ‘yan ta’addan ke rike da yankin.

“Ban yarda da ikirarin da tsohon hafsun tsaro ya yi wajen bikin yi masa sallama, da ya ce babu wani yanki a Najeriya da ke karkashin Boko Haram ba.” Inji Lawan.

Jaridar ta rahoto shi ya na cewa: “Ina cewa wannan ne domin gaba daya karamar hukumata, ta na hannun 'Yan Boko Haram na tsawon shekaru uku da su ka wuce.”

“Yanzu haka da na ke maka magana, babu wani mutum guda da ke zaune a karamar hukumata, Guzamala, abin takaici babu ko kanshin sojoji a kauye (Guzamala)."

Shekaru 3 kenan kauyenmu, Guzamala ya na hannun Boko Haram inji Rt. Hon. Lawan
Shugaban majalisar Borno Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

KU KARANTA: Da Gwamnonin APC sun tsaya sun yi aiknsu, da an samu tsaro - PDP

Ya ce kafin yanzu, a wajen wani taro da aka yi a 2020, Ministan yada labarai, Alhaji Lai Mohammed ya yi irin wannan ikirari, wanda sam ba gaskiya ba ne.

‘Dan siyasar ya ce gwamnatin nan mai-ci ta yi kokari bayan ta hau mulki, amma a cewarsa, maganar karbe ko ina daga hannun Boko Haram, ba gaskiya ba ne.

A jiya ne mu ka ji cewa ‘yan ta'addan kungiyar Boko Haram sun yi ta'adi da ya sa aka yi kwana da kwanaki babu wutar lantarki a babban birni Maiduguri, Jihar Borno.

Mutanen garin Maiduguri da kewaye su na zaune a cikin duhu bayan ‘yan ta’addan Boko Haram sun lalata wani babban layin wutarn da ya jawo lantarki zuwa jihar.

NAN ta ce abubuwa sun tsaya cak sakamakon lalata wutar lantarkin da Boko Haram su ka yi

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel