Dalilin da yasa Buratai da sauran tsoffin hafsoshin tsaro suka gaza, Wike ya fasa kwai

Dalilin da yasa Buratai da sauran tsoffin hafsoshin tsaro suka gaza, Wike ya fasa kwai

- Gwamnan Ribas ya zargi tsoffin hafsoshin tsaro da shiga siyasa, hakan ce ta sa suka kasa tabuka abun arziki

- Ya yi kira ga sabbin shugabbanin tsaron kasar nan da kada su bi sahun magabatansu in har suna son samun nasara

- Wike ya tabbatar da cewa babu musu shiga siyasa ce ta sa lamurran tsaron kasar nan suka tabarbare

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce kalubalen tsaron da aka samu karkashin tsoffin hafsoshin tsaro sun samu wurin zama ne saboda shiga siyasa da suka yi.

Kamar yadda Gwamna Wike yace, "A maimakon su mayar da hankali wurin tsaron kasar nan, shugabannin sun saka kansu ciikin siyasa."

A yayin zantawa da gidan talabijin na Channels a shirin siyasa na ranar Lahadi, Wike yayi kira ga sabbin shugabannin tsaron da kada su bi hanyar da magabatansu suka bi.

KU KARANTA: Gwamnan APC ya amince da hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, rai da rai ga masu fyade

Wike ya bayyana dalilin da yasa tsoffin hafsoshin tsaro suka samu matsala yayin aikinsu
Wike ya bayyana dalilin da yasa tsoffin hafsoshin tsaro suka samu matsala yayin aikinsu. Hoto daga @ChannelsTv
Source: Twitter

"Matsalar da muka samu da tsoffin hafsoshin tsaron shine shiga siyasa da suka yi a maimakon mayar da hankali wurin tsaron kasa.

"Babu wanda zai musanta cewa matukar aka saka siyasa a tsaro, toh tabbas za a samu matsaloli," Wike yace.

Gwamnan yace matukar sabbin hafsoshin tsaron suka bi hanyar tsoffin, babu iinda za su kai.

KU KARANTA: Ganduje ya bukaci a haramta yawon shanu daga arewa zuwa kudancin kasar nan

A wani labari na daban, wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun afka Chabal da wasu anguwanni dake karkashin karamar hukumar Magumeri a ranar Lahadi da rana sannan sun kashe wasu 'yan sanda guda biyu kafin su yi garkuwa da wasu biyu.

Kamar yadda wasu suka sanar da Vanguard, 'yan ta'addan sun kwace wasu motocin sintiri guda biyu sannan suka banka wa daya wuta a hanyar Maiduguri-Chabal-Magumeri titi mai tsawon 35km arewa da babban birnin jihar.

Al'amarin ya faru ne bayan sababbin hafsoshin sojin Najeriya da sun kai ziyara Maiduguri, inda suka kai wa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ziyara da Shehun Borno, Abubakar Garbai Elkanemi don neman hadin kansu wurin kawo karshen rikici a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel