Yadda muka kwato kananan hukumomi 20 daga hannun Boko Haram, Janar Olonisakin

Yadda muka kwato kananan hukumomi 20 daga hannun Boko Haram, Janar Olonisakin

- Mutum daya mafi matsayi a hukumar Soja, CDS Olonisakin, ya yi murabus

- Shugaba Buhari ya nada sabbin hafsoshin tsaro ranar Talata

- Tsaffin hafsoshin sun mika ragamar mulki ga wadanda zasu gajesu

Shugaban hafsoshin tsaron Najeriya mai barin gado, Janar Abayomi Olonisakin (mai ritaya), ya ce hukumar Sojoji ta kwato dukkan kananan hukumomin da yan ta'addan Boko Haram suka mamaye a baya.

Ya kara da cewa hedkwatar tsaro ya samu nasarori da dama wajen inganta lamarin tsaro, kayan aikin Soji, da kuma jin dadin sojojin da ake aiki a hedkwatar.

Yayin magana lokacin da yake mika ragamar mulki hannun magajinsa, Manjo Janar Lucky Irabor, a Abuja ranar Juma'a, Olonisakin ya zayyana irin sauyin da ya kawo hukumar.

"Za ku tuna cewa lokacin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tya hau mulki, yan ta'addan Boko Haram suna cin karensu ba babbaka a sassan Arewa maso yammacin Najeriya, inda suka mamaye kananan hukumomi 20 cikin 26 dake jihar Borno," Janar Olonisakin yace.

"Babban kalubalen da muka fuskanta lokacin da muka shiga ofis shine fitittikan yan Boko Haram tare da kwace kananan hukumomin daga hannun yan ta'addan."

"Tare da taimakon gwamnati da mutanen Najeriya, Sojojin Najeriya karkashin jagorancina sun kwace dukkan wuraren nan dake karkashin Boko Haram."

Janar Olonisakin ya ce duk da cewa akwai sauran matsalar tsaro a Najeriya, sun yi iyakan kokarinsu wajen aiki da gwamnati don dakile matsalar tsaron.

KU DUBA: Jerin sunaye: Shugabannin dakarun sojin kasa na Najeriya tun daga 1999 da jihohinsu

Yadda muka kwato kananan hukumomi 20 daga hannun Boko Haram, Janar Olonisakin
Yadda muka kwato kananan hukumomi 20 daga hannun Boko Haram, Janar Olonisakin
Source: Twitter

KU KARANTA: Na bar rundunar sojin Najeriya fiye da yadda na tarar da ita, Buratai

A bangare guda, daya daga cikin dalibai matan sakandaren Chibok, Hauwa Halim Maiyanga, ta samu yanci bayan shekaru biyar da yan ta'addan Boko Haram suka kwasheta da kawayenta.

Hauwa na cikin matan makarantan sakandaren gwamnatin mata dake Chibok, jihar Borno, ranar 14 ga Afrilu, 2014.

A cewar TheCable, wata majiya daga gidan Soja ta bayyana cewa hakan ya biyo bayan hare-haren da ake kaiwa inda aka ceto daruruwan mutanen da yan Boko Haram suka sace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel