Gwamnatin Buhari ba da gaske take yaki da rashin tsaro ba, in ji Wike

Gwamnatin Buhari ba da gaske take yaki da rashin tsaro ba, in ji Wike

- Gwamnan jihar Ribas ya bayyana cewa gwamnatin Buhari bata shirya yaki da ta'addanci ba

- A wata tattaunawa, gwamnan ya bayyana yadda siyasa ya shiga aikin sojoji da 'yan sanda

- Ya kuma bayyana cewa da gwamnatin tarayya ta shirya karar da ta'addanci da tuni ta aikata

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta da gaskiya a yakin da take yi da rashin tsaro a kasar.

Wike, wanda yayi magana a cikin shirin Siyasar gidan talabijin na Channels TV ya ce gwamnati ta sanya siyasa a yakin ta na rashin tsaro.

Ya ce, “Na farko, ya kamata ku tambayi kanku, shin Gwamnatin Tarayya tana da gaskiya? Shin da gaske suke yi wajen ganin cewa akwai tsaro a dukkan jihohin? Idan ka tambaye ni zan ce A'a.

“Dole ne mu fahimci lokacin da mutane suke wasa game da siyasa. Gwamnatin Tarayya ba ta da gaskiya game da tsaro. Abin da nake fada a yau ba sabon abu ba ne amma kuma, mutum ya yi magana ya ce wannan ba hanyar da dole ne kasar ta ci gaba ba ne.”

KU AKARNTA: Wani magidanci ya dabawa tsohuwar matarshi wuka a gaban kotu

Gwamnatin Buhari ba da gaske take yaki da rashin tsaro ba, in ji Wike
Gwamnatin Buhari ba da gaske take yaki da rashin tsaro ba, in ji Wike Hoto: The Sun News
Asali: UGC

Gwamnan ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ba ta yin abin da ya kamata don magance barazanar tsaro a jihohi.

Ya ce, “damuwarmu ita ce su tabbatar sun samar da tsaro ga kasar nan. Wannan shi ne abin da za su ce. Yanzu, ta yaya suka tabbatar sun yi tanadi don tsaron rayuka da dukiyoyin kowace jiha don mu sami amincewa da dogaro da gwamnati?

“Sojojin sun tsunduma cikin harkokin siyasa sosai. Don haka, ba zan iya gaskanta cewa Gwamnatin Tarayya da gaske take yi ba game da aikin ’yan sanda. Wannan siyasa ce kuma bana son kowa ya yaudare ni."

A kan hanyar ci gaba, Wike ya ce, “Maganar gaskiya ita ce idan har muna son kasar nan ta ci gaba, dole ne jiha ta mallaki kayan tsaro na jihohinsu.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya ƙaddamar da jami'an kula da dokar Korona 2,000

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya ce maimakon a auna shi kuma a yaba masa kan ayyukan da gwamnatin sa ke yi, manyan kasar nan sun gwammace su zage shi, ReubenAbati ya ruwaito.

Ya yi magana ne bayan cin abincin rana da gwamnonin APC bayan sake tabbatar da kasancewarsa dan jam’iyyar a mazabarsa da ke Daura, Jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel