Buhari: APC ba zata kara daurewa wani dan takara gindi daga Abuja ba
- A ranar Asabar ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sabunta rijistarsa ta zama mamba a jam'iyyar APC
- Buhari ya yi tattaki zuwa mazabarsa a garin Daura domin sabunta rijistarsa ta jam'iyya da kuma dan sararawa na kwana biyu
- Da yake magana da manema labarai, shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa lokacin cushen 'yan takara daga Abuja ya kare
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa mambobin jam’iyyarsa ta APC tabbacin cewa daga yanzu, babu wani ɗan takarar da zai sake samun goyon bayan a zabe shi daga Abuja.
Buhari ya bayar da wannan tabbaci ne a ranar Asabar yayin da yake magana da yan jarida a Daura jim kaɗan bayan kammala sake sabunta katin zama ɗan jam'iyya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Shugaban, wanda ya samu rakiyar mambobin kwamitin riko na jam’iyyar, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan; gwamnoni da sauran mambobin jam’iyyar, ya ce burinsa shi ne ya tabbatar da cewa al'umma ne ke da ta cewa cikin jam'iyyar.
KARANTA: Kura ta ci kura: An yi artabu tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu a Katsina, fiye da 100 sun mutu
Ya ce, "Babu wani lallabawa zuwa Abuja, ku bar jama'a su san cewa suke da iko a mazabunsu da jam'iyya".
Ya ƙara da cewa, "Da muka zo, mun fitar da kuɗaɗe don a biya albashi. Amma manyan ƙasar nan ba su da buƙatar hakan, sun fi son yi mana zagon ƙasa duk da ƙoƙarin da muke yi.
KARANTA: Babban sarkin kabilar Yoruba ya aika muhimmin sako ga 'yan siyasa bayan ganawa da Buhari
Shugaban, ya shawarci masu zaɓe da cewa, "Ku ne ke da ta cewa a mazabunku, ku dage ku shawo kan manya da su ba mu haɗin kan da muke mukata. Muna iya ƙoƙarinmu duk da ƙarancin kuɗaɗen."
A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke salwantar da rayukan jama'a a sassan Nigeria.
A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.
Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin wannan shekarar, 2021.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng