Sule Lamido: Saboda Buhari ake tsangwamar Fulani a Nigeria

Sule Lamido: Saboda Buhari ake tsangwamar Fulani a Nigeria

- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Buhari ne dalilin da yasa yan kudancin Najeriya ke tsangwamar Fulani

- Lamido ya ce mutane suna amfani da Buhari ne a matsayin madubin da suke kallon Fulani sai dai ba su san cewa ba dukkan Fulani ke son Buhari ba ko suka zabe shi

- Jigon na PDP ya ce rashin mulki mai kyau na gwamnatin Buhari yasa ake tsangwamar makiyaya Fulani duk da cewa hakan bai dace ba

- Har wa yau, Lamido ya yi korafi kan yadda wadanda suka taimakawa Buhari ya samu mulki a 2015 daga kudu ba su kare makiyaya duk da sun san ba kowa ne bata gari ba

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya ce ana tsangwamanr Fulani ne a Najeriya saboda Shugaba Muhammadu Buhari ya fito daga kabilar fulani ne, Daily Trust ta ruwaito.

Lamido ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis yayin da ya ke tattaunawa a kan zargin aikata laifuka da ake yi wa makiyaya Fulani a kudu maso yammacin kasar.

Sule Lamido: Saboda Buhari ake tsangwamar Fulani a Najeriya
Sule Lamido: Saboda Buhari ake tsangwamar Fulani a Najeriya. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta soke zaben dan majalisar APC a Kogi

Ana zargin makiyaya da garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da kashe Yarabawa da ke zaune a kudu maso yamma.

Rotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo, ya bawa makiyaya wa'adin kwanaki bakwai su fice daga dazukan jiharsa muddin ba su yi rajista ba inda shima ya ce ya yi hakan ne saboda tsaro.

A jihar Oyo, wani shugaban matasa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho shima ya bawa makiyayan wa'adin ficewa daga yankin Ibarapa a jihar.

Da ya ke magana kan wadannan wa'adin da aka bawa fulani, Lamido ya ce ana tsangwamar fulani ne saboda kabilarsu daya da shugaban kasa duk da cewa ba dukkansu ne suke goyon bayansa ba.

KU KARANTA: Mun gwammace mu mutu da mu bari Sarkin Fulani ya dawo Oyo, in ji mutanen Igangan

"Suna amfani da Buhari ne a matsayin madubin kallon Fulani, wanda shima Fulani ne. Sun kasa fahimtar cewa ba kowanne Fulani ne ke goyon bayan Fulani ba. Ni kai na Fulani ne amma ban zabi Buhari ba," in ji Lamido.

"Abinda ke faruwa da Fulani a kasar nan bai dace ba. Ana tsangwamar mu, ana zagin mu daka kiran mu da sunaye marasa kyau saboda Buhari dan kabilar mu ne. Hakan ba adalci bane.

"Yau idon yan Najeriya ya rufe da kiyayyar Fulani saboda mulkin Buhari mara alkibla, suna mantawa cewa ba dukkan fulani suka zabe shi ko suke son shi ba."

Lamido ya kuma dora laifi kan wadanda suka taimakawa Buhari ya samu mulki a 2015 daga yankin kudu maso yamma.

"Me yasa wadanda suka taimaka wa Buhari samun mulki a 2015 ba su kare mutanensa. Ina su Tinubu, Fashola, Amaechi, Ngige, Soyinka, Rochas da sauransu, mai yasa ba za su kare mutanen Buhari ba?" in ji Lamido.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel