Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto

Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto

- Wani da ake zargin dan fashi da makami ne ya rasa rayyuwarsa a jihar Sokoto

- Dan majalisar jam'iyyar APC ne ya bindige wanda ake zargi dan fashin ne yayinda suka yi yunkurin afka masa gida

- Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da afkuwar lamarin ta bakin kakakinta

Wani abu mai kama da wasan kwaikwayo, wani da ake zargin dan fashi da makami ne ya rasa ransa a hannun dan majalisar Nigeria, Dr Abdullahi Balarabe Salame.

Dan majalisar wakilan tarayyar na jam'iyyar All Progresive Congress, APC, ya bayyana cewa ya bindige wanda ake zargin dan fashin ne a lokacin da shi da tawagarsa suka zo kai hari gidansa a Sokoto.

Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto
Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto. Hoto: Dr Abdullahi Balarabe Salame
Asali: UGC

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Gwadabawa da Illela ya ce yan fashin sun kai masa hari ne a gidansa da ke Bado a garin Sokoto kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Ya ce:

"Dukkan godiya ya tabbata ga Allah, yau misalin karfe 3 na dare. Yan fashi sun kawo hari gida na amma da izinin Allah na bindige daya daga cikinsu har lahira na kuma raunta wasu. Ina godiya ga Allah."

Dan majalisar ya wallafa wasu hotunan a shafinsa na Facebook.

Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto
Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto. Hoto: Dr Abdullahi Balarabe Salame
Asali: Twitter

Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto
Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto. Hoto: Dr Abdullahi Balarabe Salame
Asali: Facebook

Kazalika, Rundunar yan sandan jihar ta bakin mai magana da yawunta Muhammad Sadiq ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Abdullahi Salame shine shugaban kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan rage talauci.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel