Mun gwammace mu mutu da mu bari Sarkin Fulani ya dawo Oyo, in ji mutanen Igangan

Mun gwammace mu mutu da mu bari Sarkin Fulani ya dawo Oyo, in ji mutanen Igangan

- Mutanen garin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa a jihar Oyo sun ce gara su mutu da su bari Sarkin Fulani, Abdulkadri Saliu ya dawo garin

- Mutanen garin da taimakon mai rajin kare hakkin Yarabawa Sunday Igbaho ne suke fatattaki Sarkin Fulanin da wasu makiyaya daga garin

- Mutanen garin na zargin makiyaya da aikata laifuka ne a garin don haka suka basu wa'adin ficewa daga garin kuma yanzu sun ce ba su maraba da su

- A bangarensa, Sarkin Fulani, Abdulkadri Saliu ya ce zai iya komawa garin idan har an bashi damar komawa duk da abinda ya faru a baya na korarsa

Mazauna garin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa North a jihar Oyo sun dauki alkawarin cewa ba za su sake barin sarkin Fulani da aka kora a garin, Abdulkadri Saliu, ya sake dawowa ba, The Punch ta ruwaito.

A cewarsu, barin shi ya sake dawowa garin daidai ya ke da kashe kansu da kansu, sun kara d acewa gara su mutu da su amince Saliu ya dawo garin.

Gara mu mutu da Sarkin Fulani ya dawo Oyo, mutanen Igandan
Gara mu mutu da Sarkin Fulani ya dawo Oyo, mutanen Igandan. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wadanda Buhari ya naɗa manyan hafsoshin sojoji sun cancanta, in ji Shettima

"Gara dukkan garin su kashe kansu a maimakon su bari Sarki ya dawo. Gara mu sadaukar da rayyukan mu a maimakon su bari jikokinmu da za su zo nan gaba su rayu karkashin mulkin zalinci na Sarki," jagoran kungiyar masu neman cigaban Igangan, Oladiran Oladokun ya shaidawa The Punch.

Oladokun ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke martani kan jawabin da Sarki ya yi na cewa zai iya dawowa Igangan.

"Idan an bani dama komawa garin, zan iya komawa," a cewar Saliu a ranar Alhamis, wadda iyalansa a halin yanzu sun yada zango a garin Ilorin na jihar Kwara.

DUBA WANNAN: Kotu ta soke zaben dan majalisar APC a Kogi

Tunda farko, Legit.ng ruwaito cewa fitaccen mai kare hakkin Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sundau Igboho ya zargi makiyaya da aikata laifuka a kasar Ibarapa don haka ya basu wa'adin kwanaki bakwai su fice daga garin.

Bayan cikar wa'adin shi da yaransa da wasu mazauna Igangan sun fattaki Sarkin Fulan da wasu makiyaya daga garin.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel