Shugaban kasa ya aika tawaga tun daga Abuja zuwa Kankara, ya yi zamansa a gida

Shugaban kasa ya aika tawaga tun daga Abuja zuwa Kankara, ya yi zamansa a gida

-An shiga wata Makarantar gwamnati a garin Kankara, an sace dalibai 300

-Shugaba Muhammadu Buhari ya na jihar Katsina a lokacin da abin ya faru

-A maimakon shugaban kasar ya kai ziyara, sai ya aika wakilai daga Abuja

Duk da yana garin Daura, jihar Katsina, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ki zuwa ya ziyarci Kankara, inda aka sace wasu ‘yan makaranta.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kutsa makarantar gwamnati ta kimiyya dake garin Kankara, su kayi awon-gaba da yara da-dama.

Punch tace a maimakon shugaban kasar ya tashi da kafafunsa daga garin Daura zuwa Kankara tun da ya na Katsina tun kafin abin ya faru, sai ya aika tawaga.

Buhari ya zabi wakilan gwamnatin tarayya su tashi tun daga Abuja, su tafi jihar Katsina suyi wa al’ummar da aka yi wa wannan ta’adi jaje a madadinsa.

KU KARANTA: Halin da ake ciki yau, bai kai munin na da ba - Sheikh Jingir

A ranar Lahadi, Ministan tsaro Janar Salihi Magashi (retd.), ya jagoranci shugabannin hafsun soji, su ka je garin Kankara, inda aka sace yara fiye da 300.

Wadanda ke cikin tawagar Ministan sun hada da: Janar Abayomi Olonisakin, Air Marshal Sadique Abubakar; da shugaban hukumar NIA, Ahmed Abubakar.

Jaridar ta fitar da rahoto cewa mutane da kungiyoyi sunyi tir da wannan mataki da shugaban kasar ya dauka na tura tawaga ta wakilce shi a garin da yake.

Kungiyoyi rinsu Coalition of Northern Groups; the Middle Belt Forum, Ohanaeze Ndigbo da Afenifere duk sun hadu sun yi Allah-wadai da wannan batu.

KU KARANTA: Harin Kankara: Dakarun Najeriya sun yi wa barayi zobe

Shugaban kasa ya aika tawaga tun daga Abuja zuwa Kankara, ya yi zamansa a gida
Shugaban kasa Buhari ya ki zuwa Kankara Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Shugaban kasar ta bakin hadiminsa, Garba Shehu, ya yi watsi da sukar da aka yi, ya ce abin da ke gabansu shi ne a ceto wadannan dalibai, ba a sa siyasa a ciki ba.

Dazu kun ji cewa a jihar ta Katsina, an yi fama da mugayen hare-haren miyagun ‘Yan bindiga da masu garkuwa da mutane tsakanin ranar Asabar zuwa Lahadi.

‘Yan bindiga sun hallaka wani manomi a garin Jibia, sannan an sace wani direba da mata biyu da ya dauko, yayin da shugaban kasar ya kawo ziyara zuwa mahaifarsa.

Haka zalika an kai wa wata mota hari, inda wadanda suke cikinta suka samu suka tsira da rauni.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel