Wadanda Buhari ya naɗa manyan hafsoshin sojoji sun cancanta, in ji Shettima
- Tsohon gwamnan Borno, Kashim Shettima ya jinjinawa Shugaba Muhammadu Buhari kan nada sabbin manyan hafsoshin soji
- Shettima ya ce shugaban kasar ya yi tunani sannan ya zabo mutanen da suka dace kuma kwararru da aka san su da jajircewa wurin aiki
- Sanata Shettima na daga cikin yan Najeriya da suka rika kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sauya tsaffin manyan hafsoshin sojojin
Sanata Kashim Shettima daga jam'iyyar mai APC mai wakiltar Borno Central ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya zabo mutanen da suka cancanta yayin nadin sabbin manyan hafsoshin sojoji na kasar, Daily Trust ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a Maiduguri yayin da yan jarida suka nemi jin ra'ayinsa game da nadin musamman duba da cewa makonni da suka gabata ya yi kira ga shugaban kasar ya sauya shugabannin sojojin.
DUBA WANNAN: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa
Ya ce Buhari ya dauki lokacinsa domin gano kwamandojin sojoji da suka cacanta kuma suke da ilimi kan yaki da yan ta'addan Boko Haram duba da cewa dukkansu sunyi aiki a Borno a baya.
"Shugaban kasa ya yi zabi mai kyau. Na yi mu'amala da wasu daga cikinsu kuma na tabbatar da kwarewarsu da jajircewa. Janar Leo Irabor na daga cikin kwararun babban hafsan tsaro da aka taba samu a Najeriya.
"Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Babban hafsan sojojin ruwa, ya yi aiki a Borno haka shima Janar Ibrahim Attahiru, Babban hafsan sojojin kasa ya yi aiki na kankanin lokaci," wani sashi cikin jawabinsa.
KU KARANTA: Wasu daga cikin yan matan Chibok sun sake tsere wa daga hannun yan Boko Haram
Tsohon gwamnan na Borno ya ce babu wata matsala tsakaninsa da tsaffin manyan hafsoshin sojojin sai dai ya yi kira a sauke su ne domin samun zaman lafiya a Borno da kasa baki daya.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng