Wasu daga cikin 'yan matan Chibok sun sake tsere wa daga hannun 'yan Boko Haram

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok sun sake tsere wa daga hannun 'yan Boko Haram

- Wasu daga cikin yan matan sakandare na garin Chibok da Boko Haram ta sace a 2014 sun tsere daga hannun yan ta'addan

- Sakataren kungiyar iyayen dalibai na marakantar matar ta Chibok, Lawal Zannah ya tabbatar da lamarin

- Sai dai a halin yanzu ba a tantance adadin yan matan da suka tsere daga dajin ba domin suna hannun hukuma ana tantance su

Wasu daga cikin yan matan makarantar mata ta Chibok da Boko Haram suka sace tun a shekarar 2014 sun tsere daga hannun su a yau, Daily Trust ta ruwaito.

Daya daga cikin iyayen yaran da ya yi magana da Daily trust ya ce jami'an da ke kula da yan matan sun tuntubi iyayen da abin ya shafa inda ya ce akwai yiwuwar a gayyace su Maiduguri nan gaba.

Yanzu yanzu: Wasu daga cikin yan matan Chibok sun tsere daga hannun yan Boko Haram
Yanzu yanzu: Wasu daga cikin yan matan Chibok sun tsere daga hannun yan Boko Haram. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shekau ya fitar da sabon sautin murya, ya gargadi sabbin shugabanin sojoji da Buhari ya naɗa

Wata majiya ta ce Halima Ali tana daga cikin yan matan da aka yi imanin cewa tsere shekaru biyar bayan da yar uwarta Maryam ta gudo.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an daura wa Halima aure da wani kwamanda bisa umurnin Abubakar Shekau watanni kadan bayan sace su daga makarantarsu ta kwana da ke Chibok.

An yi kokarin tuntubar mahaifin Halima amma hakan bai yi wu ba sai dai majiya kwakwara ta shaidawa wakilin Daily Trust cewa yan uwa da abokan arziki sun dunguma zuwa gidansu Halima don taya su murna.

KU KARANTA: Kuɗin ɗawainiyar jana'izar mahaifina na ke nema, matashin da aka kama da katin ATM 17

Sakataren kungiyar iyayen dalibai na makaranatar Chibok, Lawal Zannah, ya ce ya samu labarin cewa wasu daga cikin yan matan sun gudo amma bai tantance adadinsu ba.

"Mun ji cewa wasu daga cikin yan matan mu sun gudo daga cikin daji amma ba mu samu cikaken bayanin adadinsu ba," in ji Zannah.

Wasu mayakan Boko Haram ne suka sace matan su 219 daga makarantarsu a 2014 abinda ya dauki hankalin kasashen duniya.

A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.

An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.

Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel