Mutum 2 sun sheka lahira yayin da bata-gari suka yi yunkurin balle ofishin 'yan sanda

Mutum 2 sun sheka lahira yayin da bata-gari suka yi yunkurin balle ofishin 'yan sanda

- Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta tabbatar da halakar mutum biyu a yankin Akobi

- Kakakin rundunar ya sanar da yadda bata-gari suka kai wa ofishin 'yan sanda hari

- Fadeyi ya ce sun cafke biyu daga cikin bata-garin da ke tada tarzoma a yankin

Wani matashi mai shekaru 29 mai suna Badmus Rasheed a ranar Alhamis ya sheka lahira a Ibadan bayan 'yan daba sun kai hari ofishin 'yan sandan Mapo, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi ya tabbatar.

Fadeyi ya ce, tun a ranar Talata wani mutum mai shekaru 60 mai suna Module Daramola a yankin Akobi aka harbe shi da harsashi wanda aka tabbatar bata-gari ne suka aikata.

Kakakin rundunar 'yan sandan yayin bayani game da aukuwar lamarin ya ce: "Yan daba dauke da makamai daga yankin Shogoye/Akobi sun tada tarzoma. Sun raunata jama'a da dama tare da kashe wasu mutum biyu."

KU KARANTA: Shugaban marasa rinjaye tare da wasu 'yan majalisar 6 sun koma APC

Mutum 2 sun sheka lahira yayin da bata-gari suka yi yunkurin balle ofishin 'yan sanda
Mutum 2 sun sheka lahira yayin da bata-gari suka yi yunkurin balle ofishin 'yan sanda. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

Ya ce: "Bayan cafke 'yan daba biyu da suka addabi yankin, wani dan daba mai suna Packaging ya jagoranci bata-gari da za su kai 30 inda suka kaiwa 'yan sanda hari tare da sakin 'yan daban biyu da aka kama.

"A kokarin 'yan sandan na gujewa gobara, sun dinga harbi a iska."

A ranar Laraba, Fadeyi ya ce wani Akeem tare da wasu fusatattun bata-gari sun kutsa ofishin 'yan sanda don kai mummunan hari. Sun tarwatsa wasu motoci da ke farfajiyar ofishin 'yan sandan da ke Mapo.

Fadeyi yayi kira ga iyaye da su ja kunnen 'ya'yansu a kan tada tarzoma, Daily Trust ta tabbatar.

KU KARANTA: Arangamar kungiyoyin 'yan bindiga biyu ya kawo salwantar rayukan 'yan ta'adda masu yawa a Katsina

A wani labari na daban, Sarkin Musulmi na Sokoto, Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar III, a ranar Laraba ya shawarci gwamnati da kada ta matsa wa 'yan Najeriya akan riga kafin COVID-19.

Ya bayar da wannan shawarar ne yayin da yake jawabi a wani taro na limamai da malaman addini akan COVID-19 wanda aka yi a Abuja, Vanguard ta wallafa.

Sarkin ya bayar da shawarar kada a takura wa 'yan Najeriya don su amince da riga-kafin, amma a dinga ilimantar da su da kuma basu bayanai masu kyau akan cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel