Shugaban marasa rinjaye tare da wasu 'yan majalisar 6 sun koma APC

Shugaban marasa rinjaye tare da wasu 'yan majalisar 6 sun koma APC

- 'Yan majalisa shida tare da shugaban marasa rinjaye na jihar Ogun ne suka koma jam'iyyar APC

- Kakakin majalisar ya sanar da hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis a wasiku mabanbanta

- Sun ce komawarsu jam'iyyar mai mulki ya biyo bayan tuntubar shugabanni da magoya bayansu

'Yan majalisa bakwai na jihar Ogun da suka hada da shugaban marasa rinjaye, Ganiyu Oyedeji ne suka bar jam'iyyar APM zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Kakakin majalisar jihar, Olakunle Oluomo, ya bayyana haka a wasu wasiku mabanbanta da ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Alhamis a Abeukuta, babban birnin jihar, Punch ta wallafa.

Wadanda suka sauya shekar baya da Oyedeji: Musefiu Lamidi (Ado Odo Ota 11), Yusuf Amosun (Ewekoro), Sikiratu Ajibola (Ipokia), Bolanle Ajayi (Yewa South), Adeniran Ademola (Sagamu 11) da Modupe Mujota-Onikepo (Abeokuta North).

KU KARANTA: Dangote: Yadda tsohuwar budurwata ta so 'warwarar' $5m daga wurina

Shugaban marasa rinjaye tare da wasu 'yan majalisar 6 sun koma APC
Shugaban marasa rinjaye tare da wasu 'yan majalisar 6 sun koma APC. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Sabbin hafsoshin tsaro: NGF tayi martani, ta sanar da Buhari abu 1 da ya dace yayi

A wasiku mabanbanta na 'yan majalisaru, sun ce sun yanke shawarar komawa jam'iyyar APC bayan tuntubar shugabanninsu da magoya bayansu.

A martanin kakakin majalisar, ya taya 'yan majalisar murna da suka koma jam'iyyar mai mulki tare da cewa hakan yana da matukar amfani domin ganin cigaban jihar baki daya.

Oluomo ya yi kira ga shugaban marasa rinjaye na majalisar da ya dauka babban matakin komawa jam'iyya mai mulki.

Bayan sauya shekar a yau, APC tana da mambobi 22 daga cikin 26 na majalisar. ADC tana da mambobi 3 sai PDP da ke da 1.

A wani labari na daban, Sarkin Musulmi na Sokoto, Alh. Muhammad Sa'ad Abubakar III, a ranar Laraba ya shawarci gwamnati da kada ta matsa wa 'yan Najeriya akan riga kafin COVID-19.

Ya bayar da wannan shawarar ne yayin da yake jawabi a wani taro na limamai da malaman addini akan COVID-19 wanda aka yi a Abuja, Vanguard ta wallafa.

Sarkin ya bayar da shawarar kada a takura wa 'yan Najeriya don su amince da riga-kafin, amma a dinga ilimantar da su da kuma basu bayanai masu kyau akan cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel