Wike da Gwamnonin Jihohin Arewa sun ji dadin nada sababbin Hafsun tsaro

Wike da Gwamnonin Jihohin Arewa sun ji dadin nada sababbin Hafsun tsaro

- Kungiyar Gwamnonin Arewa ta yaba da nadin sababbin hafsun Sojojin kasa

- Shugaban kungiyar, Gwamna Simon Lalong, ya fitar da jawabi a ranar Laraba

- Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya jinjinawa Buhari a kan wannan nadi

Kungiyar gwamnonin jihohin Arewa ta yi farin ciki da shugaba Muhammadu Buhari ya nada sababbin shugabannin tsaro, AIT ta fitar da wannan rahoto.

Wannan kungiya ta gode wa tsofaffin hafsun sojojin da irin gudumuwar da su ka ba kasarsu.

Jawabin gwamnonin ya fito ne ta bakin shugabansu, Simon Bako Lalong, inda ya gode wa shugaban kasa, ya kuma yi kira ga wadanda aka zaba, su dage.

A cewar Simon Bako Lalong, jama’a su na sa ran sababbin hafsun sojojin za su kawo zaman lafiya, a dalilin haka ne ya yi kira gare su, ka da su ba mutane kunya.

KU KARANTA: A 2020 Buhari ya fara kyankyasa cewa zai yi nadin sababbin hafsoshi

Shugaban kungiyar gwamnonin na Arewa ya nemi shugabannin tsaron su kawo karshen garkuwa da mutane, ta’addanci da hare-haren miyagun ‘yan bindiga.

Gwamna Lalong ya ce gwamnonin Arewa za su ba wadannan hafsun soji da aka nada goyon bayan da su ke bukata na shawo kan matsalolin yankin da na kasa.

A ranar Talata ne Nyesom Wike na jihar Ribas ya jinjina wa shugaba Muhammadu Buhari na sauraron kukan mutane, ya dauki wannan mataki na kawo canji.

Vanguard ta ce gwamnan ya yi magana ne ta bakin kwamishinansa na sadarwa da yada labarai, Paulinus Nsirim, ya yi kira ga hafsoshin su kawo zaman lafiya.

KU KARANTA: Buhari ya yi watsi da dokoki a nadin shugabannin tsaro – Kungiya

Wike da Gwamnonin Jihohin Arewa sun ji dadin nada sababbin Hafsun tsaro
Hafsun sojojin da aka nada Hoto: Facebook @FemiAdesina
Asali: Facebook

Wike ya ce ko da nadin ya zo a makare, ya fi ace ba ayi ba. Gwamnan ya yi kira a ba hafsoshin hadin-kai, su yi aiki, sannan ya yi kira ka da su biye wa ‘yan siyasa.

A makon nan ne aka yi waje da Janar Abayomi Olonisakin; Laftana Janar Tukur Buratai; Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas; da kuma Air Marshal Sadique Abubakar.

Shugaban kasar ya maye gurabensu ne da Manjo Janar Leo Irabor, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, Rear Admiral Awwal Gambo Zubairu, Air Vice Marshal I.O. Amao.

Wike ya nuna godiyarsa ga tsofaffin hafsun sojojin da aka maye gurabensu bayan shekaru biyar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel