Bikin su Atiku ya hada Tinubu, Kwankwaso, Ganduje da El-Rufai a cikin rumfa daya

Bikin su Atiku ya hada Tinubu, Kwankwaso, Ganduje da El-Rufai a cikin rumfa daya

- A karshen makon nan ne Aliyu Atiku Abubakar ya auri Fatima Nuhu Ribadu

- Manyan mutanen da ake ji da su da-dama sun samu halartar wannan taro jiya

- Gwamnoni, Sanatoci, Ministoci da tsofaffin masu mulki duk sun halarci bikin

A ranar Asabar, 3 ga watan Satumba, 2020, aka daura auren Alhaji Aliyu Atiku Abubakar da kuma Fatima Nuhu Ribadu a babban birnin tarayya Abuja.

Turakin Adamawan ya angonce da ‘diyar tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, kuma daya daga cikin manyan ‘yan siyasar jiharsu ta Adamawa.

Kamar yadda Legit.ng ta samu labari, manyan ‘yan siyasa daga duka jam’iyyun da su ka yi fice a Najeriya sun halarci wannan gagarumin biki da aka yi.

Manyan APC, Bisi Akande da Bola Tinubu su na cikin gawurtattun ‘yan siyasar da su ka samu halartar daurin auren ‘ya ‘yan na Atiku da Malam Ribadu.

KU KARANTA: Hotunan auren 'Dan tsohon mataimakin shugaban kasa da Ribadu

Daga jihar Adamawa bikin ya samu halartar manyan ‘yan siyasa irinsu tsohon gwamna, Murtala H. Nyako, da Gwamnan yanzu Ahmadu Umaru Fintiri

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da tawagarsa ta ‘yan Kwankwasiyya; Abba Kabir Yusuf da irinsu Abdullahi Baffa Bichi sun je bikin.

Haka zalika ba a bar gwamnan jihar Kano mai-ci, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a baya ba.

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya na cikin gwamnonin da su ke wajen wannan taro. Sauran takwarorinsa sun hada da Aminu Tambuwal, Kayode Fayemi.

KU KARANTA: Atiku zai iya takara a 2023 - PDP

Bikin su Atiku, Tinubu, Kwankwaso, Ganduje da El-Rufai a cikin rumfa daya
Wajen bikin Aliyu Atiku da Fatima Ribadu Hoto: BBC
Asali: UGC

Sanatoci irinsu Aliyu Wammako da jagororin siyasar jihar Gombe; Muhammad Danjuma Goje, Hassan Dankwambo da Inuwa Yahaya duk sun je bikin.

Ragowar wadanda su ka je bikin su ne: Ministan sadarwa, Isa Ali Pantami, Muazu Babangida Aliyu, Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni da sauransu.

Kafin nan kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje auri Hajiya Aminatu Dahiru, shugabar kamfanin nan na Binami, ranar Juma’a.

Manyan kusoshin gwamnati a Najeriya sun samu halartar wannan auren a garin Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel