Buratai: Sai godiya, Obasanjo ya kusa sallamata ta daga aiki shekaru 21 da su ka wuce

Buratai: Sai godiya, Obasanjo ya kusa sallamata ta daga aiki shekaru 21 da su ka wuce

- Janar Tukur Buratai ya mikawa sabon hafsun sojojin kasa shugabancin gidan soja

- Tukur Buratai yace an kusa yi masa ritaya daga aiki a lokacin gwamnatin Obasanjo

- Olusegun Obasanjo ya yi wa wasu sojoji rututu ritaya bayan ya karbi mulki a 1999

Tsohon shugaban hafsun sojan kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai, ya ce Olusegun Obasanjo ya kusa yi masa ritaya shekaru fiye da 20 da su ka wuce.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya yana cewa tsohon shugaban kasar ya nemi ya yi masa ritaya ne a lokacin ya na Manjo.

Da yake jawabi a ranar Alhamis, Tukur Buratai, yace ya kafa tarihi da ya kai kolin aikin gidan soja, ya kuma ya samu damar kai wa matsayin Laftanam-Janar.

Janar Buratai mai ritaya ya yi wannan jawabi ne a hedikwatar sojojin kasa da ke Abuja, lokacin da ya ke mika ragamar gidan soja ga sabon hafsun sojin kasa.

KU KARANTA: Buhari ya keta dokar kasa a nadin hafsun sojoji

Tsohon hafsun sojan kasar yake cewa: “Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kusa ya sallame ni daga aiki shekaru 21 da suka wuce, a lokacin ina manjo.”

“Ritayar da na yi bayan shekaru 40 a aiki abin tarihi ne, don haka akwai bukatar ayi godiya.”

Yayin da yake jawabi wajen mika ragamar gidan soja ga Manjo Janar Ibrahim Attahiru, Buratai ya ce ya kawo canji sosai a tsawon shekaru biyar da ya yi a kan kujera.

A cewar Buratai, gidan soja ya canza har abada saboda irin nasarorin da aka samu a lokacinsa. Tsohon hafsun yace ya kawo makamai, ya habaka kwarewar sojoji.

KU KARANTA: Hafsun Sojoji: Shekau ya aiko da sabon saƙon gargadi

Buratai: Sai godiya, Obasanjo ya kusa sallamata ta daga aiki shekaru 21 da su ka wuce
Laftana-Janar Buratai da Obasanjo Hoto: This Day/Punch
Asali: UGC

TY Buratai ya ce za a tuna da shi a matsayin wanda lokacin shugabancinsa, jami’an sojoji su ka ji dadi.

A jiya ne mu ka ji cewa kungiyar Gwamnonin Arewa ta yaba da nadin sababbin hafsun Sojojin kasa, Gwamna Simon Lalong, ya fitar da jawabi a madadin kungiyar.

Bayan haka, gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ta bakin kwamishinan yada labaransa, ya jinjina wa shugaba Muhammadu Buhari a kan wannan nadi da ya yi.

Wike ya fada wa sababbin hafsun sojojin da aka nada sai sun ajiye siyasa a gefe domin su samu nasara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng