Najeriya fa kamar mota ce mara direba, Wole Soyinka

Najeriya fa kamar mota ce mara direba, Wole Soyinka

- Farfesa Soyinka ja jaddada matsayarsa kan shugabanci a Najeriya

- A cewar Soyinka, ba cutar Korona ta haifar da matsalolin da ake ciki ba

- Ya ce rashin ingantaccen shugabanci ne babban matsalan Najeriya

Shahrarren ma'abocin kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya siffanta shekarar 2020 a matsayin shekara mafi cike da kalubale saboda irin matsalolin da Najeriya ta tsinci kanta.

Ya kara da cewa halin da Najeriya ta shiga ya tsananta sakamakon rashin shugabancin kwarai daga wajen yan siyasa da Malaman addini.

Soyinka, wanda yayi jawabi a Booksellers, inda ya gabatar da sabon littafinsa da ya kwashi shekaru 40 yana rubutawa, rahoton Punch.

Sunan littafin ‘Chronicles of the happiest people on earth,’ (Jerin mutane mafi farin ciki a duniya).

"Dubi ga irin rikice-rikicen da suka faru a 2020, abubuwa basu yi dadi ba. Wannan shekarar na yi cikin mafi muni da na san kasar nan," Soyinka yace.

"Abubuwa sun kai matakin da baka san idan za ka je ka tsira ko za ka mutu ba. Kamar yadda na fada, ba zaka yarda akwai wani shugaba a kasar nan ba."

KU DUBA: An nemi Buhari an rasa a majalisa yau Alhamis

Najeriya fa kamar mota ce mara direba, Wole Soyinka
Najeriya fa kamar mota ce mara direba, Wole Soyinka
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta rage kudin 'Data' da kashi hamsin (50%), Pantami ya sanar

Watanni biyu da suka gabata, wasu manyan masu fada aji a Najeriya sun yi ittifakin cewa Najeriya ta zama kamar mota maras matuki kuma duk mota mara mai juyata hadari za tayi.

Wadannan mutanen sun hada da babban faston katolikan, John Cardinal Onaiyekan; tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega; Dr Hakeem Baba Ahmed da Janar Martin Luther Agwai (mai murabus).

Sauran sune Jibrin Ibrahim, Dr. Nguyan Shaku Feese, Dr. Usman Bugaje, Adagbo Onoja, Amb. Fatima Balla, Ambassador Zango Abdu, Auwal Musa Rafsanjani, da Chris Kwaja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng