Ba Buhari ke sarrafa sha'anin mulki ba a Aso Rock - Wole Soyinka
Fitaccen marubuci dan Najeriya, Farfesa Wole Soyinka ya ce bai yarda Shugaba Muhammadu Buhari ne ke juya akalar mulki a kasar ba.
Da ake hira ta da shi a ranar Alhamis a PlusTv Africa, marubucin ya ce abinda zai magance matsalolin Najeriya shine rage karfin da gwamnatin tarayya ke da shi tare da karfafa
Ya kuma kara da cewa akwai bukatar mutane su fahimci tarihin inda kasa ta fito da inda aka dosa, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Soyinka yana martani ne a kan budediyar wasikar da Umar Dangiwa, tsohon gwamnan soji na jihar Kaduna ya aikewa Buhari inda ya yi magana kan yadda shugaban kasar ke son nada mutanen da suka fito daga yankinsa mukami.
"Da farko, na yi mamakin ganin yadda aka yi shiru bayan fitowar wannan wasikar. Ina ganin ya dace a hukunta wadanda suka aikata wannan abin.
"Ba wai a tautauna a kan batun ba kawai ayi shiru, domin wannan laifi ne mai zaman kansa," in ji Soyinka.
"Na taba fadin haka a baya, Ban amince akwai wani takamamen wanda ke sarrafa sha'anin mulki a Aso Rock ba. Na dade ina nazarin wannan lamarin na tsawon shekara daya da rabi kuma na gamsu cewa shugaban kasa ba shi ke juya akalar mulkin kasar nan ba.
"A bangarori da fanoni da dama, na gamsu cewa ba shine ke tafiyar da kasar baki daya ba.
"Abin ya wuce yadda ake tsamani, kowa ya san wannan tarihin. Mun san abinda ya janyo a kasar nan kuma mun san bai wuce ba. Kuma kawai ka ce ka umurci ayi bincike a kan lamarin. Wannan bai wadatar ba, mutumin nan ba shi ke mulkin kasar nan ba."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng