Hotuna: Buhari ya yi ganawar farko da sabbin hafsoshin rundunonin tsaro

Hotuna: Buhari ya yi ganawar farko da sabbin hafsoshin rundunonin tsaro

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da sabbin hafsoshin rundunonin tsaro a karon farko bayan sanar da nada su

- A ranar Talata ne shugaba Buhari ya sallami dukkan tsofin hafsoshin rundunar tsaron da ya fara nadawa tun bayan hawansa mulki a 2015

- Buhari ya sha suka da korafi a wurin 'yan Nigeria akan cigaba da aiki da tsofin hafsoshin bayan cinye wa'adinsu da lokacinsu na aiki

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gana da sabbin hafsoshin rundunar soji a karon farko bayan sanar da nadinsu a ranar Talata, 26 ga watan Janairu, 2021.

Buhari, a jawabinsa, ya zaburar da sabbin hafsoshin rundunar tsaro a kan kishin kasa yayin ganawarsu ta farko ranar Laraba a fadar shugaban kasa.

"Muna cikin yanayin tsananin bukatar mafita. Ku zama masu kishi, ku hidimatawa kasa, kasa zaku yi wa aiki," a cewar Buhari kamar yadda kakakinsa, Garba Shehu, ya wallafa.

Buhari ya cigaba da cewa; "Babu wani da zan fada muku dangane da aikinku domin a cikinsa kuke.

"Ni ma a cikinsa nake, amma zan tayaku da addu'a. Sannan, ina mai tabbatar muku cewa zan baku duk wata gudunmawa da kuke bukata domin jama'a su yabawa kokarinku.

"Kun san halin da muke ciki a shekarar 2015, sannan kun san halin da muke ciki yanzu ta fuskar tsaro.

"Mun dauki alkawarin samar da tsaro, farfado da tattalin arzikin kasa da yaki da cin hanci da rashawa. Babu wanda zan ce ya kasance abu mai sauki, amma dai, tabbas an samu cigaba.

Ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai ritaya), ne ya jagoranci hafsoshin rundunonin sojin zuwa wurin taron.

KARANTA: Ka daina shararawa 'yan Nigeria karya; Dan majalisa ya caccaki ministan Buhari

Sabbin hafsoshin sun hada da babban hafsan rundunar tsaro, Manjo Janar Leo Irabor, babban hafsan rundunar sojojin kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru.

Sauran sun hada da babban hafsan rundunar sojojin sama, Air Vice Marshal IO Amao, da takwaransa rundunar na sojojin ruwa, Rear Admiral AZ Gambo.

KARANTA: NDLEA: Marwa zai farfado da tsohuwar rundunar atisaye domin yaki da kwaya a Nigeria

Fadar shugaban kasa, a ranar Talata, na cewa abinda yasa aka sallami hafsoshin tsaro ba saboda sun gaza bane.

Ta kara da cewa an yi hakan ne a wannan lokacin domin kara karfi a fannin yaki da ta'addanci tare da shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan.

Femi Adesina, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a fannin yada labarai, ya sanar da hakan a wata zantawa da yayi da Channels TV a kan siyasa kuma Punch ta kiyaye.

Hotuna: Buhari ya yi ganawar farko da sabbin hafsoshin rundunonin tsaro
Hotuna: Buhari ya yi ganawar farko da sabbin hafsoshin rundunonin tsaro
Source: Facebook

A kwanakin baya Legit.ng ta rawaito shugaban kasa, Muhammadu Buhari, na cewa ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke salwantar da rayukan jama'a a sassan Nigeria.

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu jiga-jigan dalilai guda hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin bayan kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a cikin wannan shekarar, 2021.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel