PDP ta ce akwai bukatar a gudanar da bincike a kan tsofaffin Hafsun Sojoji

PDP ta ce akwai bukatar a gudanar da bincike a kan tsofaffin Hafsun Sojoji

- Mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu bayan an nada sababbin Hafsun tsaro

- Jam’iyyar hamayya ta PDP ta bukaci a binciki tsofaffin Hafsun Sojojin Najeriya

- Wasu sun ce shugabannin tsaron da aka yi, su na da laifuffukan da za su amsa

Jama’a su na cigaba da magana a game da nadin sababbin hafsun sojojin da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a ranar Talata da yamma.

Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta yi maza ta yi martani bayan fadar shugaban kasa ta sanar da nadin shugabannin tsaro, ta ce an riga an makara tun tuni.

A cewar PDP, shugaban kasar bai nada sababbin hafsun sojojin a lokacin da ya kamata ba, ya bar tsofaffin shugabannin sun dade a ofis har tsaro ya tabarbare.

Jam’iyyar hamayyar ta kuma bukaci gwamnati tarayya ta binciki duka tsofaffin hafsun sojoji.

KU KARANTA: Hafsun Sojoji: Akwai yiwuwar wasu manyan Sojoji su je gida su huta

“PDP ta bukaci ayi gaggawan gabatar da bincike a game da wa’adin tsofaffin shugabannin tsaron da aka cire domin gano inda aka samu matsala a harkar tsaro.”

Jawabin na PDP ya na cewa wannan bincike zai taimaka wajen bankado gaskiyar zargin satar kudin da aka ware domin sayen makamai da alawus domin sojoji.

Da yake magana a madadin PDP, Kola Ologbondiyan, ya ce wannan bincike ne kawai zai karfafa kwarin gwiwar dakarun sojojin da ke yaki a filin daga a Najeriya.

Sahara Reporters ta rahoto cewa wasu sun fito shafin Twitter su na rokon a kai tsofaffun hafsun sojojin kasan gaban babban kotun Duniya na ICC domin a bincike su.

KU KARANTA: Buratai zai mika ragamar gidan Soja ga wanda ya gagara kamo Shekau

PDP ta ce akwai bukatar a gudanar da bincike a kan tsofaffin Hafsun Sojoji
Ana kiran a binciki hafsoshin tsaro Hoto: Twitter: @hqnigerianarmy
Asali: Twitter

Masu wannan kira sun zargi sojoji da aika-aikan da su ka hada da kisan gillar ‘Yan shi’a a Zaria, jama’a a garin Orlu da Oyigbo, hallaka ‘yan zanga-zanga a Lekki.

A na sa bangaren, shugaban kasa ya yaba da aikin tsofaffin hafsun, ya ce ba gaza wa ta sa aka sallame su ba.

Kun san cewa hafsun sojojin da aka yi wa ritaya su ne: Abayomi Gabriel Olonisakin Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ibas da kuma Air Marshal Sadique Abubakar.

An maye guraben su ne a jiyan da Manjo Janar Lucky Irabor; Manjo Janar Ibrahim Attahiru; Rear Admiral A.Z Gambo, da kuma Air-Vice Marshal Isiaka Amao.

A dalilin wannan, ana tunanin za a yi wa jami’an Sojoji akalla 20 ritaya domin su ba wasu wuri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng