COVID-19: An tsawaita umarnin da aka ba Ma’aikata na dakatar da zuwa ofis

COVID-19: An tsawaita umarnin da aka ba Ma’aikata na dakatar da zuwa ofis

- An umarci ma’aikatan gwamnati su cigaba da yin aiki daga cikin gidajensu

- Gwamnatin tarayya ta bada wannan umarni ne saboda matsalar COVID-19

- Sanarwar ta ce ma’aikatan za su koma zuwa ofis a karshen watan Fubrairu

A makon nan gwamnatin tarayya ta bada umarni ga wasu ma’aikatanta su tsaya a gidajensu, su cigaba da aiki daga can, ba tare da sai sun zo ofis ba.

Jaridar The Cable ta ce wannan umarni ya zo ne a wata sanarwa da gwamnatin tarayya ta yi ta bakin shugaban ma’aikatan kasar, Folasade Yemi-Esan.

Misis Folasade Yemi-Esan ta fitar da takarda inda ta aika wa fadar shugaban kasa, majalisar tarayya, da kuma sakatarorin din-din-din na ma’aikatu.

Folasade Yemi-Esan ta bayyana cewa daukar wannan mataki ya zama dole ne domin takaita yaduwar cutar COVID-19 da ta ke ta harbin Bayin Allah.

KU KARANTA: Buhari ya nada Aghughu Adolphus a matsayin Mai binciken kudi

Takardar ta ce duka ma’aikatan tarayya da ke kan matsayi na 12 zuwa abin da ya yi kasa, su cigaba da zama a gida zuwa karshen watan Fubrairun 2021.

Ga abin da jawabi ya ce:

“Bayan takarda mai lamba HCSF/3065/Vol.1/47 da mu ka aiko a ranar 22 ga watan Disamba, 2020, a kan wannan batu bisa shawarar kwamitin yakin COVID-19 na PTF, duka ma’aikatan da ke kan mataki na GL 12 zuwa kasa za su cigaba da aiki daga gida, zuwa karshen Fubrairu.”

KU KARANTA: NGF, Miyetti Allah sun yarda, za a fara yi wa Makiyaya rajista

COVID-19: An tsawaita umarnin da aka ba Ma’aikata na dakatar da zuwa ofis
Dr. Folasade Yemi-Esan Hoto: www.sunnewsonline.com
Source: UGC

Yemi-Esan ta yi kira ga manyan sakatarori da shugabannin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya su tabbatar ma’aikata sun bi umarnin.

Jawabin na Yemi-Esan ya ke cewa: “Ya na da muhimmanci a jaddada bukatar bin wannan sharuda da aka shimfida domin dakile yaduwar COVID-19.”

A makon nan ne mu ka samu labari cewa Kasar Amurka ta tallafa wa Najeriya da ginin wani katafaren asibiti na musamman da za a rika kebe masu COVID-19.

Ofishin tsaron Amurka na reshen Afrika ne ya yi wannan abin-a-yaba, tare da hadin-gwiwar kungiyar USAID, da cibiyar kula da cututtuka da hukumar WRAIR.

Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard da Ministan lafiya, suka bude wannan asibiti wanda ya ci Dala miliyan 1.3 a unguwar Jabi da ke cikin garin Abuja.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel