Da dumi-dumi: Buhari ya naɗa Aghughu a matsayin sabon AGF
- Buhari ya amince da bada Mista Aghughu Adolphus a matsayin babban auditan tarayya
- Shugaban ya aike da takardar nadin ga majalisar dattawa domin tantancewa
- Adolphus, dan asalin jihar Edo shine ke rike da mukamin tin bayan ritayar Anthony Ayine biyo bayan cikar sa shekara 60
Shugaba Kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Aghughu Adolphus a matsayin babban mai binciken kudaden na gwamnatin tarayya, AGF, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Shugaban ya mika takardar nadin ga shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan kamar yadda sashe na 86 (1) na kundin tsarin mulki ya tanada.
DUBA WANNAN: An kama matasa 'Hausawa' dauke da bindigu a Oyo
A wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja, mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin majalisa, Sen. Babajide Omoworare ya ce Aghughu ne ke rike mukumin tun bayan ritiyar Mr. Anthony Mkpe Ayine daga aiki bayan cikarsa shekara 60, ranar 25 ga Oktobar 2020.
KU KARANTA: Kada su sake ku kusanci dazukan mu, 'Yan kabilar Ijaw sun gargadi makiyaya
Sabon auditan ya fito daga Jihar Edo, ya na da digiri na biyu a tsimi da tanadi (Economics), dan kungiyar Association of National Accountants of Nigeria, mamba ne a Nigerian Institute of Management da kuma Chartered Institute of Taxation.
Ya zama audita a ofishin babban audita a 1992 kuma an kara masa girma zuwa daraktan binciken kudi (Director of Audit) a Janairun 2016.
Idan za a iya tunawa shugaba Muhammadu Buhari a cikin watan Disambar 2016, ya mika sunan Ayine don maye gurbin Florence Anyanwu da ke rike da mukamin a lokacin a matsayin rikon kwarya.
An mika sunan Ayine wata shida bayan tsohon babban auditan tarayya, Samuel Ukuru ya ajiye aiki.
A wani labarin daban, Hukumar Kula da Makarantun Frimare, SUBEB, ta Jihar Kaduna ta sanar da sallamar wasu malaman firamare 65, kamar yadda Kamfanin dillancin labarai na NANS ya ruwaito.
An ruwaito cewa an dauke su ba bisa ka'ida ba a karamar hukumar Sanga da ke jihar kamar yadda Premium Times ta wallafa. Gwamnatin Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki.
Jami'in binciken SUBEB, Tandat Kutama, wanda ya rike sakataren kwamitin bincike, ya tabbatar wa da NAN rahoton a Kaduna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng