Rikicin Makiyaya: Bakin Kungiyar Miyetti Allah da Gwamnoni sun zo daya

Rikicin Makiyaya: Bakin Kungiyar Miyetti Allah da Gwamnoni sun zo daya

A ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021, shugabannin Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria suka gana da kungiyar gwamnoni na NGF.

An yi wannan zama ne domin shawo kan sabanin da aka samu tsakanin makiyaya da gwamnatin jihar Ondo da ta ba masu kiwo wa’adi su bar cikin jeji.

Gwamnonin Yarbawa: Rotimi Akeredolu; Gboyega Oyetola; Dr. Kayode Fayemi; Seyi Makinde da kuma irinsu Mohammed Badaru da Atiku Bagudu sun halarci taron.

Jaridar Punch ta rahoto cewa za a rika yi wa makiyaya rajista domin a kawo karshen ta’adin da ake samu.

Mun tattaro maku matsayar da aka cin ma a karshen wannan zama da aka yi:

KU KARANTA: Rikicin Makiyaya: Yadda za a samu mafita - Bukola Saraki

1. Sha’anin tsaro matsalar kasa ce wanda ta shafi kowace kabila da addini da ya kamata a hada kai domin a shawo kanta.

2. ‘Yan jarida sun juya abin da gwamnan Ondo ya fada da ya ce Makiyayan da ke cikin kungurmin jeji su tashi.

3. Dole a kama duk masu laifi, a hukunta su, ba tare da la’akari da addini, kabila ko matsayinsu ba.

4. Akwai bukatar hadin-kai tsakanin kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria da jami’an tsaro.

5. Babu wasu mutane da aka fatattaka daga jihar a Najeriya.

6. An haramta kiwo cikin duhun dare daga yanzu.

7. Barin kananan yara suna kiwo ya na da hadari, an haramta hakan.

8. An yi tir da zama da tare wa da wasu ke yi a cikin kungurmin daji wanda ya saba doka.

9. Mutanen Miyetti Allah suna fama da matsalar garkuwa da mutane da sauran matsolin tsaro.

10. Kungiyar Miyetti Allah a shirye ta ke, ta taimaka wa jihohi wajen shawo kan matsalar rashin tsaro.

Rikicin Makiyaya: Bakin Kungiyar Miyetti Allah da Gwamnonin sun zo daya
Gwamnoni a taron jiya Hoto: Twitter Daga: @SeyiMakinde
Source: Twitter

KU KARANTA: Buhari bakin-jini kurum ya jawo mana - Miyetti Allah

11. Dole a dakatar da kiwo a fili domin kawo karshen rikicin makiyaya da manoma.

12. Kungiyar makiyaya ta MACBAN tana goyon bayan a kawo dabarun kiwo na zamani da nufin hana dabbobi yawo.

13. Za a kafa kwamiti da zai kunshi jami’an gwamnati, manoma, ‘Yan Miyetti Allah a jihohin da babu (kwamitin) domin a cin ma nasara.

A jiya kun ji cewa aika-aikar wasu miyagun Makiyaya ta sa dole Jagororin Fulani sun nemi gafara wajen taro da aka gudanar a jihar Oyo a ranar Lahadi.

Makiyayan da suke ta’adi sun tatsi N50m daga garkuwa da mutane da su ke yi a yankin Iganga, jihar Oyo, hakan ya sa manyan Fulani su ka ba Jama’a hakuri.

Sarkin Fulanin kasar Igbo Ora da Sarkin Fulani Eruwa sun nemi afuwa a bakacin makiyaya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel