Sabbin hafsoshin tsaro: An riga an gama aika-aika ga tsaron kasa, PDP
- Jam'iyyar PDP ta kwatanta canja shugabannin tsaro da Buhari yayi a matsayin abinda ya kamata yayi tun tuni amma ya ki yi sai yanzu
- A ranar Talata sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan, ya ce wajibi ne a bincika tsofaffin shugabannin tsaron sosai don a gano inda suka saka kudade
- Ya zarge su da almundahana da ha'inci, a cewarsa zai yuwu suna da hannu a kwashe kudaden da aka ware don walwalar sojoji na filin daga
Jam'iyyar PDP ta kwatanta canja tsofaffin shugabannin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari yayi a matsayin makararren mataki, don jama'a sun riga sun cutu, Daily Trust ta ruwaito.
PDP ta bukaci a yi gaggawar bincike akan yadda tsofaffin shugabannin tsaron suka tafiyar da ayyukansu lokacin da suke kan kujerunsu, saboda tana zargin suna da hannu dumu-dumu akan satar kudaden da aka ware musamman don tabbatar da walwalar rundunoni a filayen daga.
A wata takarda ta ranar Talata, sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya ce "Daga baya kenan, sadaka da karuwa. A cewarsa sun riga sun janyo rikicewar kasa da asarar rayuka."
KU KARANTA: Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40
PDP ta ce "Tsofaffin shugabannin tsaron mutane ne marasa kishi da tausayin kasa, basu damu da duk asarorin rayuka da aka yi ba da kuma shiga halin rintsi da kuma fatara kuma duk Buhari yana zaune yana kallo."
"Da a ce Buhari ya dauki mataki tun lokacin da jam'iyyarmu ta shawarce shi da ya cire su, da asarar rayukan basu kai haka ba.
"Muna fatan hakan zai zama izina ga Buhari ya dinga daukar shawarwari masu amfani ba ya dinga barin kasar mu tana shiga halin ha'ula'i ba kafin yayi gyara.
"Sai dai jam'iyyarmu tana fatan za a samu gyara sakamakon canja shugabannin tsaron da aka yi wurin kawo karshen tashin hankali da matsalolin tsaro dake addabar kasar nan."
KU KARANTA: Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata
A wani labari na daban, a kalla rai daya aka rasa yayin da wasu suka jigata a ranar Talata sakamakon arngamar 'yan sanda da 'yan kungiyar shi'a na Najeriya.
Lamarin ya faru a yankin Maitama da ke babban birnin tarayya da ke Abuja kusa da hukumar kula da hakkin dan Adam ta kasa.
A yayin da zanga-zangar tayi kamari, 'yan sandan sun dinga harbi tare da watsa barkonon tsohuwa domin tarwatsa 'yan shi'an, lamarin da ya kai ga kisan mutum daya a take.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng