Dalilin da yasa Buhari ya sallami hafsoshin tsaro, Fadar shugaban kasa
- Fadar shugaban kasa ta ce ba saboda gazawa bane aka ssallami tsoffin hafsoshin tsaro ba
- An sallamesu ne saboda ana bukatar sabbin jini kuma da sabbin dabarun yaki
- Buhari ya jinjinawa tsoffin hafsoshin tsaron ta yadda suka bautawa kasar nan
Fadar shugaban kasa a ranar Talaa ta ce abinda yasa aka sallami hafsoshin tsaro a yau ba saboda sun gaza bane. Ta kara da cewa an yi hakan ne a wannan lokacin domin kara karfi a fannin yaki da ta'addanci tare da shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan.
Femi Adesina, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman a fannin yada labarai, ya sanar da hakan a wata zantawa da yayi da Channels TV a kan siyasa kuma Punch ta kiyaye.
"Abinda yasa suka tafiya a yau ba yana nufin sun gaza bane. A gaskiya ba hakan bane. Kawai ana son sabbin jini ne da kuma sabbin dabarun yaki a kasar nan," yace yayin da yake sanar da jinjinar da Buhari yayi wa tsoffin shugabannin tsaron.
KU KARANTA: Ba ki cancanci a aure ki ba idan namiji yana magana kina mayarwa, Budurwa ga tsagerun mata
"A takardar da shugaban kasar ya fitar a yau Talata, ya jinjinawa hafsoshin tsaron da suka tafi a kan gudumawar da suka bada wurin tsaron kasar nan. Ya gamsu da ayyukansu ba kadan ba.
“Wadannan da suke tafiya a yau sun kasance a kujerunsu na tsawon shekaru biyar da watanni biyar. Lamarin na yin abinda ya dace ne a lokacin da ya dace," Adesina ya kara da cewa.
KU KARANTA: Kafintan da matansa suka haifa yara 4 a mako 3 yace burinsa ya haifa yara a kalla 40
A wani labari na daban, jam'iyyar PDP ta kwatanta canja tsofaffin shugabannin tsaro da shugaba Muhammadu Buhari yayi a matsayin makararren mataki, don jama'a sun riga sun cutu, Daily Trust ta ruwaito.
PDP ta bukaci a yi gaggawar bincike akan yadda tsofaffin shugabannin tsaron suka tafiyar da ayyukansu lokacin da suke kan kujerunsu, saboda tana zargin suna da hannu dumu-dumu akan satar kudaden da aka ware musamman don tabbatar da walwalar rundunoni a filayen daga.
A wata takarda ta ranar Talata, sakataren yada labaran jam'iyyar, Kola Ologbondiyan ya ce "Daga baya kenan, sadaka da karuwa. A cewarsa sun riga sun janyo rikicewar kasa da asarar rayuka."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng