Uzodinma: COVID-19 ta na harbin mutane, al’umma su na ta mutuwa a Imo

Uzodinma: COVID-19 ta na harbin mutane, al’umma su na ta mutuwa a Imo

- Hope Uzodinma ya ce Coronavirus ta na ta hallaka Bayin Allah a Jihar Imo

- Gwamnan ya bayyana cewa za a fara kama wadanda ba su rufe fuskokinsu

- Uzodinma ya kai ziyara Aso Villa ya na neman tallafin gwamnatin tarayya

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya fito gaban Duniya ya na koka wa game da yadda cutar COVID-19 ta ke kashe mutane a kwanakin nan.

Sanata Hope Uzodinma ya ce yawan masu dauke da kwayar Coronavirus a jihar Imo ya na tashi sama.

A sanadiyyar yaduwar cutar, mutane suna ta mutuwa, wannan ya sa gwamnatin Hope Uzodinma ta fito da matakai da za su tsare rayukan sauran al’umma.

Uzodinma ya shaida wa manema labarai cewa daga yanzu za a rika hukunta duk wanda aka samu da laifin kin rufe fuska kamar yadda doka ta ce.

KU KARANTA: Sojoji sun yi wa ‘Yan bindiga rugu-rugu a dajin Zamfara – inji DHQ

Gwamnan ya ce Imo na ganin tasirin sabon samufurin kwayar COVID-19 da ya bayyana, don haka ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo masa agaji.

Mai girma gwamnan ya yi wannan bayani ne bayan ya kai ziyara Aso Villa, ya gana da Muhammadu Buhari ranar Litinin, 18 ga watan Junairu, 2021.

“Masu kamuwa da COVID-19, kuma suke mutuwa a jihar Imo ya na karu wa. Maganar gaskiya, gwamnatin jiha kadai ba ta da ikon da za ta shawo kan annobar.”

“Saboda haka na roki shugaban kasa, kuma ya yi alkawarin zai taimaka mana.” Inji Uzodinma.

Uzodinma: COVID-19 ta na harbin mutane, al’umma su na ta mutuwa a Imo
Gwamna Uzodinma da Shugaba Buhari Hoto: www.pulse.ng/news/local
Asali: UGC

KU KARANTA:

A cewarsa, ya sa hannu a dokar da za ta takaita yaduwar COVID-19. “Na bada wa’adin kwanaki 14 ga duk masu shigowa Imo, su bi umarnin NCDC ko a cafke su.”

Duk da an kafa kotu shida da dakunan ajiye masu jinya hudu, adadin masu cutar ya karu. Gwamnan ya ce dole sai an yi da gaske, sannan a kawo masu dauki.

A farkon makon nan mu ka ji labari cewa kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF ta kira taro na musamman bayan Coronavirus ta harbi mutane fiye da 112, 000.

Kamar yadda Abdulrazaque Bello-Barkindo ya bayyana, gwamnonin kasar za suyi zama ne domin ganin yadda za a rage yaduwar Coronavirus a fadin jihohi.

Kayode Fayemi da Ifeanyi Okowa za su yi wa Gwamnoni jawabi a wajen wannan taro da za ayi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel