Ortom: Benuwai ke gaba na, ba ni da sha’awar fitowa takarar Shugaban Najeriya a zaben 2023

Ortom: Benuwai ke gaba na, ba ni da sha’awar fitowa takarar Shugaban Najeriya a zaben 2023

- Wasu sun fito su na ta rokon Samuel Ortom ya nemi Shugaban kasa a 2023

- Gwamna Ortom ya bayyana cewa sam ba wannan buri ne ke gabansa yanzu ba

- Hadimin Gwamnan ya nemi magoya baya su nesanta shi daga siyasar kasa

Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya yi kira ga mabiyansa su guji alakantasa da shiga takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2023.

Jaridar Punch ta bayyana cewa Samuel Ortom ya yi wannan kira ne a ranar Litinin dinnan.

Gwamna Samuel Ortom ya shaida wa mutanensa cewa bai da niyyar ya tsaya neman takarar shugaban kasa kamar yadda wasu su ke ta rokon shi ya fito.

Wasu mutane a shafukan sada zumunta sun fito da tambarin “Project Ortomise Nigeria Ortomatically 2023” su na rokon Ortom ya nemi shugaban kasa.

KU KARANTA: Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu a 2023 ba - Sule Lamido

Wani mutumi mai suna Samuel, ya fito dandalin Facebook ya na yi wa gwamna Ortom yakin zabe tun yanzu, ya ce shi ne zai iya hada kan duk kabilun kasar nan.

“Najeriya ta na bukatar mutum maras kabilanci, jajirtaccen jagora irin gwamna Samuel Ortom, wanda a shirya yake ya kare mutanen Najeriya da karfi da ikonsa.”

Sakataren yada labaran gwamnan Benuwai, Terver Akase, ya yi magana, ya ce Ortom yana ganin darajar magoya da kungoyin masoyansa, amma ba ta wannan yake ba.

Mista Terver Akase ya ce abin da ke gaban mai gidansa shi ne yi wa mutanen jihar Benuwai aiki.

KU KARANTA: 'Dan El-Rufa'i ya nuna yiwuwar mahaifinsa da Tinubu su yi takara a 2023

Ortom: Benuwai ke gaba na, ba ni da sha’awar fitowa takarar Shugaban Najeriya a zaben 2023
Gwamna Ortom Hoto: Punch.ng
Asali: UGC

“Har yanzu Ortom yana da shekaru biyu da rabi da zai cika a wa’adinsa na gwamna, kuma ya sadaukar da kansa wajen kara yi wa jiharsa hidima ne.” Inji Akase.

A watan jiya ne tsohon shugaban kasan Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya yi bayani a kan batun da ake yi na cewa ya na da niyyar sake tsaya wa takara a 2023.

Goodluck Jonathan ya ce ya kamata a maida hankula a kan wasu matsalolin da ke addabar kasa.

Ganin cewa har yanzu ana 2020 ne, Jonathan ya ce ya yi wuri da za a fara bayyana burin tsayawa takara.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng