Dakarun Amotekun sun yi ram da wani gawurtaccen ‘Dan fashi a Jihar Ondo

Dakarun Amotekun sun yi ram da wani gawurtaccen ‘Dan fashi a Jihar Ondo

- Dakarun Amotekun sun kama wani hatsabibin barawo a Jihar Ondo

- Wannan mutum ya tabbatar da cewa ya yi fashi a gidaje fiye da 100

- Bayan haka ya kwanta da mata sama da 50 ta hanyar surkule da asiri

Dakarun jami’an tsaron da aka kirkira a jihohin Kudu maso yammacin Najeriya wanda aka fi sani da Operation Amotekun sun kama wani hatsabibi.

Ana tuhumar wannan mutum mai suna Shina Adaramola mai shekara 46 da laifuffukan da suka hada sata a garin Owo, karamar hukumar Owo, jihar Ondo.

Da ake yi masa tambayoyi, wannan mutum da ake tunanin magini ne, ya ce ya yi fashi a gidaje fiye da 100, sannan ya yi wa mata sama da 50 fyade.

Punch ta rahoto cewa wannan mutum ya kan yi amfani da siddabaru ne wajen aikata wannan aika-aika.

KU KARANTA: Aika-aikar Miyagu ta sa dole Jagororin Fulani sun nemi gafara

Ya ce: “Ina zama a Ijare, ina da wadda zan aura da ta tafi ta bar ni, ta samu wani mutum, ana saura ‘yan kwanaki kadan mu yi aure. Wannan ya fusata ni.”

A cewarsa, wannan ya sa ya shiga fashi da makami, domin ya ga ana samun kudi a harkar.

“Da zarar za a yi bidirin casu, sai in yi kamar ina cikin masu shirya bikin. Ina da wani irin kayan bude kwalbar giya wanda na ke bude kwalaben attajirai. Haka na ke yi.”

“Na dade ina yin wannan aiki, tun da na rasa komai a Duniya, mai gidana ya kore ni in bar gidansa, matar da zan aura ta tsere, tace babu abin da na ke da shi.” Inji sa.

KU KARANTA: Masoya sun zo dandalin Twitter, an tuna soyayyar da aka caba

Dakarun Amotekun sun yi ram da wani gawurtaccen ‘Dan fashi a Jihar Ondo
Motocin Dakarun Amotekun Hoto: www.businessday.ng
Asali: UGC

“Na yi wa mata kimanin 50 fyade. Duk lokacin da zan kwanta da mace, ina bari ne sai cikin dare, sai in yi amfani da asiri. Na kan tabbatar na rufe wa mace baki.”

Shugaban Amotekun na shiyyar, Cif Adetunji Adeleye, ya ce sune su ka yi ram da wannan mutum.

Jiya kun ji cewa rundunar 'yan sanda na reshen jihar Katsina ta yi bajakolin wasu dumbin 'yan bindiga da tarin makamai da aka kama a makon an.

An kama wani mutum mai suna Haruna Yusuf, ɗan jamhuriyar Nijar, wanda ake zargin da safara tare da sayar da makamai ga masu garkuwa mutane a yankin.

A daidai wannan lokaci kuma an cafke uba da ƴaƴan sa biyu a cikin gungun 'yan bindiga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng