Soyayya: Labarin kyauta, sadaukar da kai da Maza su kayi wa Matan Twitter
Wasu ‘yan matan Arewacin Najeriya da aka fi sani da ‘Yan Arewa Twitter sun bada labarin soyayyar da suka yi da samarinsu wanda yanzu sun rabu, ko sun aure su.
Wani matashi mai suna Haidar, ya fara jefa wannan tambaya a shafinsa na Twitter, inda aka samu mata da-dama su ka rika fada wa Duniya irin soyayyar da su ka zabga a da.
Haidar ya tambayi ‘yan matan ko an taba yi masu abin da har suka ji za su auri samarin na su.
Wata mai suna Ummi Lolo ta ce wani ya taba yin tafiyar kilomita 991 domin ya gan ta, amma a karshe ziyarar ta kare da hawaye.
Wata matar aure ta tuna da soyayyar da ta ci a budurci, ta ce ba za ta ce komai ba, domin kuwa yanzu Ubangiji ya yi ta auri masoyin na ta.
KU KARANTA: Budurwa ta yi garkuwa da tsohon saurayinta
Ita ma wata matar auren ta ce: “Ya yi mani duk abin da namiji zai iya yi wa mace.” Ta ce wannan Bawan Allah ya sadaukar da rayuwarsa a kanta, sai godiya.
Malama Aysha Mahmud ta ce ko da sun rabu da wannan mutumi, amma ya koya mata tashi cikin dare domin ta yi sallah.
Wata kuwa cewa ta yi akwai saurayin da ta yi wanda ake biyansa albashi ta asusun bankinta.
Hafsat Paki ta ce: “Ya yi tafiya zuwa wuri mai nisa wajen daurin aure, sai ya kamo hanya ya dawo bayan nayi muhimmin rashi, ya zo ya yi mani ta’aziyya, ya koma washegari.”
A cewar Malama, Zainab Muhammad, ta taba hadu wa da wani mai godiya da hakuri da fahimta.
KU KARANTA: Ta rabu da maigidanta, ta auri 'dan sa
Wata babarbariya ta ce: “Wannan mutumi ya yi mani abubuwa da yawa. Allah yayi ni ba matar shi bace kawai.
Irinsu Amal Ahmad, Aisha Saminaka da Zainab Saminaka duk sun fito sun yabi mazan Arewa.
Kun ji labarin wata matar aure da aka garkame mijin ta a kurkuku ta bukaci kotu ta raba auren su saboda ba zata iya jira har ya fito daga gidan yarin ba.
Matar tace tun da fari an mata karyar lokacin da mijin ta zai shafe a kurkuku. Ta ce bata son saba wa ubangiji kafin a sallami mijin nata daga kaso.
Alkalin kotun da ake wannan zama a Kasuwar Nama, garin Jos, ya yi maza ya raba auren na ta.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng