Gobara ta kama masana'antar kera allurar rigakafi mafi girma a duniya

Gobara ta kama masana'antar kera allurar rigakafi mafi girma a duniya

- Gobara ta kama wani bangaren inda ake kera allurar rigafin kwayoyin cuta a Indiya

- Hukumar kashe gobara ta bayyana cewa ta ceto mutane uku daga gobarar

- Hukumar ta bayyana tana ci gaba da kokarin shiga yankin ginin don ceto wasu

Wata babbar gobara ta tashi a ranar Alhamis, a harabar kamfanin kera allurar kwayar cuta ta Serum ta Indiya, SII, a garin Pune na Indiya.

Gobarar ta fara ne da rana a yankin Manjari na harabar SII, babban jami’in kashe gobara na Pune, Prashant Ranpise ya fada. Ya kara da cewa an tura jami’an kashe gobara 15 zuwa wurin.

Ranpise ya ce kawo yanzu an ceto mutane uku daga ginin.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta shirya tallafawa yara 10m da ba sa makaranta

Gobara ta kama wani ɓangare a masana'antar kera allurar rigakafin Indiya
Gobara ta kama wani ɓangare a masana'antar kera allurar rigakafin Indiya Hoto: Daily Nigerian
Source: UGC

"Hukumarmu na dubawa idan wasu mutane sun makale.

"Ba mu san abin da ya haddasa gobarar ba ko kuma irin asarar da aka yi ba tukuna," in ji shi.

NDTV News duk da haka, ta ruwaito tana ambaton majiyar SII cewa wutar ba ta shafi masana'antar kera Covishield ba, rigakafin COVID-19 wanda aka ba da izinin gaggawa ta mai kula da magunguna na Indiya.

Cibiyar ta Serum tana ɗaya daga cikin manyan masu yin allurar rigakafi a duniya.

A cewar Babban Jami'in kamfanin, Adar Poonawalla, SII na shirin kera allurai kimanin biliyan daya na COVID-19 a shekara mai zuwa.

KU KARANTA: Gwamna Kebbi Bagudu ya ware N464m don tallafawa mata a jihar

A wani labarin, Kwana daya kacal bayan lafawar gobarar da ta tafka barna a babbar kasuwa Sokoto, 'yan jari bola sun mamaye kasuwar domin tsintar duk wani abu da wuta ta lalata.

Wakilin Daily Trust da ya ziyarci ksuwar ya tabbatar da cewa ya ga daruruwan 'yan jari bola suna tsintar kayayyaki suna zubawa a cikin buhunhunansu da ke cikin amalanke masu kafa biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel