Mai garin Radda da ‘Yan bindiga su ka yi awon-gaba da shi ya kira ‘Yanuwansa ta waya

Mai garin Radda da ‘Yan bindiga su ka yi awon-gaba da shi ya kira ‘Yanuwansa ta waya

- Kabir Umar Radda ya yi waya da mutanen gidansa bayan an yi garkuwa da shi

- Mai Garin na Radda ya shaida wa ‘Yanuwansa cewa ya na wani jeji a Zamfara

- Alhaji Radda ya ce ‘Yan bindigan da su ka sace shi ba su yi masa wani rauni ba

Mai garin Radda, Alhaji Kabir Umar, wanda aka sace a ranar Juma’a, 22 ga watan Junairu, 2021, ya fito ya yi magana daga inda ake tsare da shi.

Jaridar Katsina Post ta fitar da rahoto cewa wannan Basarake ya yi wa ‘yanuwansa magana, ya tabbatar masu da cewa ya na nan kalau cikin koshin lafiya.

Wani 'dan uwan wannan Bawan Allah, Mustapha Radda ya shaida wa ‘yan jarida cewa Alhaji Kabir Umar Radda ya kira mutanen gida a wayar salula.

Kamar yadda majiyar ta bayyana, Kabir Umar Radda ya yi waya da ‘yanuwan na sa ne tun a ranar Juma’a da aka dauke shi da kimanin karfe 8:00 na dare.

KU KARANTA: Mutanen gari sun kashe masu garkuwa a Katsina

Basaraken ya tabbatar masu da cewa bayan an dauke shi, an wuce da shi zuwa wani daji a jihar Zamfara, amma bai iya bayyana takamaimen inda yake ba.

Wannan mutumi ya taki sa’a, domin kuwa ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan ba suyi masa lahani ba.

Mustapha ya ce: “Ya iya zuwa da wayar salularsa, saboda haka ya kira mu, ya ce wadanda su kayi garkuwa da shi ba su taba shi ba, sun kai shi wani jeji ne a Zamfara.”

Har zuwa lokacin da wannan Mai gari ya tuntubi ‘yanuwansa, masu garkuwa da shi ba su bayyana abin da za a biya a matsayin kudin fansa domin ya fito ba.

KU KARANTA: An kashe wasu 'Yan bindiga a Kaduna

Mai garin Radda da ‘Yan bindiga su ka yi awon-gaba da shi ya kira ‘Yanuwansa ta waya
Shugaban kasa da Sarkin Katsina Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Ana yawan sulale wa da mutanen da aka dauke daga Katsina zuwa Zamfara, inda ‘yan bindiga su ke ta’adi.

An dauke Kabir Radda ne a tsakar daren Juma’ar da ta wuce, da kimanin karfe 2:00 a fadarsa da ke garin Radda, karamar hukumar Charanchi, jihar Katsina.

Wajen yin garkuwa da wannan basarake, ‘yan bindiga sun ji wa ‘danuwansa, Aminu Umar Radda, rauni a cinya, yanzu ya na jinya a wani asibiti da ke jihar Kano.

DCL ta ce mazauna garin koke-koke kawai su ke yi bayan wannan samame da ‘yan bindiga suka kai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel