Wasanni: Gwaji ya nuna Zinedine Zidane ya na dauke da kwayar COVID-19
- Gwaji ya nuna cewa Zinedine Zidane ya kamu da cutar Coronavirus
- Sanarwar kulob din ta ce Kocin zai kilace kansa sai ya samu sauki
- Real Madrid ta na cikin matsala bayan ta rasa wasu wasanni a jere
Mai horas da ‘yan wasan kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane, ya kamu da COVID-19 kamar yadda kulob din ya bada sanarwa a ranar Juma’ar nan.
Gwajin da aka yi ya tabbatar da cewa Zinedine Zidane ya na dauke da kwayar cutar COVID-19.
“Kungiyar kwallon kafan Real Madrid ya na sanar da cewa gwaji ya nuna mai horas da ‘yan wasanmu, Zinedine Zidane, ya kamu da cutar COVID-19.”
Real Madrid ta yi wannan sanarwa ne a shafinta.Kocin zai killace kansa na wani lokaci, kuma ba zai samu jagorantar kungiyar zuwa wasan Asabar ba.
KU KARANTA: Benzema zai amsa laifi a kotu
AFP ta ce kungiyar za tayi kokarin tattaro duk wasu wanda kocin ya tuntuba a lokacin da ake zargin wannan cuta ta murar mashako ta shiga jikinsa.
Jaridar ta rahoto cewa mataimakin mai horas da ‘yan kwallon Real Madrid, David Bettoni, ya na cewa Zinedine Zidane ya nan kalau bayan gwajin ya fito.
David Bettoni ya ce: “Na yi magana da kocin da safiyar nan, kuma kalau ya ke.”
“Ya na takaicin bai cikinmu da safen nan. Ba zai rabe mu ba, amma mun san ya na goyon bayanmu; zai karfafa wa ‘yan kwallon da kowa kwarin-gwiwa."
KU KARANTA: 'Yan wasan da su ka yi ritaya a shekarar 2020
Wannan sanarwa da kungiyar tayi ya na zuwa ne kwanaki biyu bayan Real Madrid ta yi abin kunya a gasar Cope Del Rey, karamin kulob ya yi waje da ita.
Ku na da labari cewa bayan nan Atletico Bilbao ta yi waje da kungiyar Madrid daga gasar Super Cup, ta yi gaba ta doke Barcelona a wasan karshe, ta lashe kofi.
A karshen shekarar 2020 bara, Alaves ta samu galaba a kan Real Madrid, amma tun bayan nan kungiyar ra rasa wasanni har aka sallami koci, Pablo Machin.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng