Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna

Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna

- Hedkwatar tsaro ta kasa ta tabbatar da halaka wasu 'yan bindiga da sojin sama suka yi a Jihar Kaduna

- Ta sanar da yadda sojin saman suka ragargaji 'yan bindigan a dajin Chikwale na karamar hukumar Chikun

- An yi wa 'yan bindigar luguden wuta bayan an gansu suna tunkarar Jihar Neja sanye da bakaken kaya

Hedkwatar tsaro ta dakarun sojin Najeriya ta ce sojin sama na rundunar Operation Thunder Strike ta ragargaza 'yan bindiga masu tarin yawa a dajin Chikwale da ke yankin Mangoro na karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

John Enenche, shugaban fannin yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan a wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi.

Enenche mai mukamin Manjo Janar, ya ce an yi ragargazar ne bayan samamen da suka kai bayan bayanan sirrin da suka samu na zaman 'yan bindigan a yankin babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, Premium Times ta wallafa.

DUBA WANNAN: Muna samun nasara a yaki da ta'addanci da 'yan bindigan daji, Sojin Najeriya

Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna
Nasara daga Allah: Dubun wasu 'yan bindiga ta cika a dajin Chikwale da ke Kaduna. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: UGC

"Kamar yadda ya dace, bayan jerin dubiya da aka yi ta jiragen yaki, sojin saman sun je a jiragen yaki inda suka ragargaji yankin.

"Yayin da dakarun sojin saman suke sintiri ta jiragen yaki, sun hango 'yan bindigan masu tarin yawa, wasu a kan babura kuma sanye da bakaken kaya suna tunkarar Jihar Neja.

"A don haka ne jiragen yakin suka dinga sakarwa 'yan bindigan ruwan wuta duk da an ga 'yan bindigan na kokarin harbo jiragen yakin," yace.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta bayyana ranar komawa makarantun gaba da sakandare na jihar

Enenche ya kara da cewa, an halaka da yawan 'yan ta'addan yayin da wasu suka tsere da miyagun raunika.

Ya kara da cewa, ana cigaba da sintiri ta jiragen yaki tare da hadin guiwar dakarun tudu don halaka 'yan bindigan da suka tsere.

Ana cigaba da samun manyan nasarori a fannin tsaron kasar nan ta yadda dakarun soji ke halaka 'yan ta'adda.

A wani labari na daban, a ranar Alhamis rundunar sojin Najeriya tace tana samun nasarori, kuma tana dab da kawo karshen ta'addanci da rashin tsaro a kasar nan.

Kakakin rundunar soji, Manjo janar John Enenche ya sanar da hakan a wani taro a Abuja. Enenche ya bayar da misalin yadda suka ci karfin ta'addanci a Jihar Zamfara da Katsina.

A wata takarda ta ranar Litinin, Enenche ya sanar da yadda rundunar Operation Hadarin Daji ta kashe a kalla 'yan bindiga 35 a jihar Zamfara a karon batta guda biyu da suka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ngng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel