Mutanen gari sun kashe masu garkuwa a Katsina
- Mazauna kauyen Unguwar Gambo sun halaka wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne
- Ganau ba jiyau ba ya tabbatar da cewa, daya daga cikin masu garkuwa da mutanen ne ya tabbatar da cewa sun sace wani yaro
- Sai da mai garkuwa da mutanen ya kai jama'ar inda yaron da aka sace yake, sannan jama'ar kauyen suka halaka su
Jama'ar kauyen Unguwar Gambo da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina sun kashe wasu 'yan bindiga wadanda da ba a san yawansu ba.
Wasu mazauna yankin sun sanar da jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya auku a ranar Lahadi yayin da daya daga cikin wadanda ake zargin dan bindiga ne ya bayyana sunan wadanda suke hada kai wurin aika-aikar.
DUBA WANNAN: Bidiyo: Sojoji sun tarwatsa mafakan shugabannin 'yan bindiga Damina da Sani Mochoko a dajin Kuyambana a Zamfara
"Abinda ya faru shine, akwai wani mutum da aka yi garkuwa da dan sa kuma sai da ya biya kudin fansa ya karba dansa.
"Daga nan cikin kwanakin sai aka sake sace wani dan sa wanda jama'ar kauyen suka dinga addu'a tare da yanka domin neman taimakon Allah.
"A ranar Lahadi, wani mutum ya fito inda ya bayyana cewa yana daya daga cikin masu garkuwa da mutanen kuma ya sanar da sauran abokan aika-aikarsa. Daga nan ne jama'a suka damkesu tare da halaka su," in ji majiyar.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina
Wata majiya wacce ta bada labari kamar yadda ta farko ta bada, ta kara da cewa, mutumin ya bayyana inda suka kai yaron kuma an dauko shi.
Jama'ar kauyen sun kashe wasu 'yan bindigar yayin da wasu ke asibitin Kwandala da ke garin Malumfashi.
A wani cigaba makamancin hakan, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa sa wani mai dakin siyar da magani a kauyen Dayi da ke karamar hukumar Malumfashi.
Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, 'yan bindigar sun zo a babura sannan suka fasa wata hanya ta bayan gidan mamacin inda suka shiga tare da fito da shi.
Ya ce 'yan sanda da 'yan sa kai sun yi kokarin ceto mutumin, amma 'yan bindigar sun yi awon gaba da shi bayan musayar wuta da suka yi.
A yayin da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin a Dayi amma ya ce har yanzu bai samu bayani game da na kauyen Unguwar Gambo ba.
A wani labarin daban, kun ji cewa an yi garkuwa da wani tsohon sojan Amurka, Manjo Jide Ijadare (mai murabus) da wani mutum guda a masana'antarsa na sarrafa manja da ke Ijan-Ekiti a karamar hukumar Gbonyin da ke jihar Ekiti.
An ruwaito cewa yan bindiga su bakwai ne suka kai farmaki a masana'antar a ranar Talata misalin karfe 2 na rana inda suka harbe wani ma'aikacinsa guda har lahira kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng