Yanzu haka: Ƴan Boko Haram na can sun kai hari a garinsu Gwamna Zulum a Borno
- An samu rahotanni da ke cewa ƴan bindiga na nan sun kai hari Mafa, garinsu Gwamna Zulum
- Majiyoyi sun ce jami'an tsaro suna can suna fafatawa da yan ta'addan don dakile harin
- Ɗaruruwan mutanen garin suna ta tsere wa suna shiga daji don tsira da ransu daga harin da 'yan ta'addan suka kawo
Wani rahoto da ba a tabbatar da sahihancinsa ba ya nuna cewa wasu ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari Hedkwatar Ƙaramar Hukumar Mafa a Jihar Borno, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.
Rahoton ya ce yan ta'addan suna can suna musayar wuta da jami'an tsaro.
DUBA WANNAN: Sojojin Nigeria 7 sun gamu da ajalinsu a hannun 'yan bindiga a dajin Nasarawa
Arewa maso gabashin Mafa ne garinsu Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum.
Garin na da nisan kimanin kilomita 40 daga Maiduguri babban birnin Jihar Borno.
KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Kaduna ta kori malamai 65 daga aiki
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce daruruwan mutane suna ta tserewa suna shiga daji domin tsira da ransu a yayin da sojoji ke ƙoƙarin ɗakile harin.
A wani labarin nan daban, Gwamnatin Jihar Kano ta umurci ma'aikatanta a jihar su zauna gida a matsayin wani mataki na dakile yaduwar annobar korona karo na biyu a jihar, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta kuma bada umurnin rufe dukkan gidajen kallo da na yin taro a jihar sakamakon karuwar adadin masu dauke da kwayar cutar COVID 19 a jihar.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da sabbin dokokin yayin taron manema labarai da ya kira a ranar Talata inda ya ce an dauki matakin ne yayin taron masu ruwa da tsaki da aka yi a ranar Litinin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng