COVID-9: Kada ka yi wasa da rayukan mutanenka, Kungiyar NGF ta gargadi wani babban gwamnan Nigeria

COVID-9: Kada ka yi wasa da rayukan mutanenka, Kungiyar NGF ta gargadi wani babban gwamnan Nigeria

- Kungiyar NGF tana al’ajabin kin amincewa da alurar rigakafin korona da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yaki yi

- Shugaban kungiyar, Gwamna Kayode Fayemi, ya gargadi Bello da ya dauki lamarin da muhimmanci

- Gwamna Kayode ya ce maimakon watsi da lamarin, kamata yayi gwamnan Kogin yayi duk abunda zai iya don tsiratar da mutanensa

Rikon sakainar kashin da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yayiwa bukatar rigakafin korona a kasar ya sanya damuwa a zukatan takwarorinsa.

Harma, Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) Gwamna Kayode Fayemi, ya gargadi Bello kan cewa kada yayi wasa da rayukan al’umman jiharsa.

KU KARANTA KUMA: FG ta bayar da sabon bayani kan shirin bayar da tallafin kudi ga matasa (kalli lambobin wayar kowani yanki)

COVID-9: Kada ka yi wasa da rayukan mutanenka, Kungiyar NGF ta gargadi wani babban gwamnan Nigeria
COVID-9: Kada ka yi wasa da rayukan mutanenka, Kungiyar NGF ta gargadi wani babban gwamnan Nigeria Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: UGC

Gwamnan na jihar Ekiti, a yayinda ya bayyana a wani shirin Channels TV, ya bayyana matsayar Bello a matsayin abun korewa kuma mai hatsari.

Fayemi ya bayyana cewa yayinda gwamnan na Kogi ke da yanci kan ra’ayinsa game da rigakafin, amma dole a baiwa kariyar mutanensa muhimmanci.

Ya kara da cewa duba ga halin da cutar ke ciki a yanzu a Najeriya, ya kamata gwamnoni su yi aiki kai da fata tare da gwamnatin tarayya domin samun mafita mai dorewa.

KU KARANTA KUMA: COVID-19: NCDC ta rahoto karin mutum 1,964 sun harbu da cutar

A gefe guda, Gwamatin tarayya ta hannun majalisar kolin tattalin arzikin Najeriya watau NEC, ta bada dama a kirkiro magungunan cutar COVID-19 a gida.

Jaridar The Nation ta fitar da rahoto a ranar Alhamis, 21 ga watan Junairu, 2021, cewa an yi hurumi a fito da magungunan COVID-19 a Najeriya. Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kuma bayyana cewa kofa a bude ta ke ga mutanen kasashen waje su shigo da maganin COVID-19 cikin kasar nan.

Fadar shugaban kasa ta ce majalisar NEC wanda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yake jagoranta tayi zama a jiya ta yanar gizo.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng