Hadimin Shugaban kasa ya tsokano fadan ‘Yan adawa da ya tabo Atiku Abubakar

Hadimin Shugaban kasa ya tsokano fadan ‘Yan adawa da ya tabo Atiku Abubakar

- Bashir Ahmaad ya tsokano wa kansa surutu a sakamakon taba Atiku Abubakar

- Magoya bayan Atiku sun yi kamar su cinye Hadimin shugaban kasar a Twitter

- Ahmaad ya yi magana mai harshen damo bayan Atiku ya taya Joe Biden murna

Hadimin shugaban kasar Najeriya, Bashir Ahmaad, ya jawo abin magana da ya tsokani tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Bashir Ahmaad wanda ya na cikin masu taimaka wa Muhammadu Buhari wajen yada labarai, ya yi wa Atiku martani bayan ya taya Joe Biden murna.

A jawabin da Alhaji Atiku Abubakar ya yi, ya roki sabon shugaban kasa Biden, ya cire takunkumin da aka sa wa ‘Yan Najeriya na zuwa Amurka.

Malam Bashir Ahmaad ya yi wuf ya yi magana a kaikaice, ya fada wa Atiku Abubakar cewa: “Duk mun gane abin da ka yi a nan, Alhaji.”

KU KARANTA: Bayan ‘yan sa’o’i kadan a kan kujera, an bijiro maganar tsige Biden

Magana mai harshen damo?

Ga wadanda ba su san abin da ya faru ba, a zaben 2019 ne Atiku Abubakar ya yi takara da mai gidan Ahmaad, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

A wancan lokaci an zargi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku da cewa idan ya shiga Amurka za a kama shi, saboda zarginsa da ake yi da aikata laifi.

Jam’iyyar APC da hadiman shugaban kasa sun taso Atiku a kan wannan maganar domin kashe masa kasuwar siyasa, a karshe Atiku ya taka kafa a Amurka.

Bayan Ahmaad ya yi wannan magana a Twitter, magoya-bayan Atiku sun yi masa ca, har ya yi wa wani martani ya nemi magani tun da abin ya yi masa zafi.

KU KARANTA: Hadimin Buhari sun hadu da Yaron Atiku a Twitter

Da yake ba wata amsa, Ahmaad ya nuna cewa Joe Biden (da aka taya murna) ya fi tsohon shugaban kasa Donald Trump sanin duk abin da Atiku ya aikata.

A jiya ne ku ka ji cewa Atiku Abubakar ya gabatar da kokon bara a madadin ‘Yan Najeriya bayan Joe Biden da Kamala Harris sun hau kan karagar mulki a Amurka.

Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, Atiku ya na neman alfarma uku a hannun Gwamnatin Biden; daga ciki a bada damar ziyartar kasar wajen.

Haka zalika Atiku ya yi kira ga sabon shugaban kasar ya kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel