Kada ku sa mu yadda cewa wadanda aka lallasa a zaben 2019 ne suka bullo da EndSARS - Hadimin Buhari ga dan Atiku
- Hadimi na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi wa Aliyu Atiku martani a kan Endsars
- A wata wallafa da dan tsohon mataimakin shugaban kasan yayi, ya zargi Endsars da komawa juyin juya hali
- Babu kakkautawa hadimin shugaban kasan ya zargi wadanda aka lallasa a zaben 2019 da samo sabon salo
Dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Aliyu Atiku Abubakar, ya yi wallafar da ta janyo cece-kuce a shafinsa na Twitter.
Wallafar kuwa ya yi ta ne a kan wannan zanga-zanga ta kawo karshen SARS wacce ta ki ci balle cinyewa.
A wallafarsa, "Juyin juya hali ne ke gabatowa a gagarumar kasar nan da ta fi kowacce kasa yawan mutane a Afrika. Wannan zanga-zanga ta EndSARS ta wuce kawo gyara ga ayyukan 'yan sanda."
Wannan wallafar babu shakka ta janyo maganganu tare da hankulan jama'a a kafar sada zumuntar zamanin.
Ba a dade da yin wallafar ba hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi martani.
Kamar yadda yace, "Kuna ta wallafa cewa zanga-zangar nan ta fi karfin bukatar gyaran ayyukan 'yan sanda a wannan manhajar. Kada ku sa mu yadda cewa wadanda suka shirya wannan zanga-zangar sune wadanda aka lallasa a zaben 2019 amma suka cire tsammanin za su samu wata dama da ta wuce juyin juya hali."
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan daba dauke da makami sun kai wa masu zanga-zanga hari a Abuja
KU KARANTA: EndSARS: Kun riga kun samu nasara, kada ku bari ta subuce - Yahaya Bello
A wani labari na daban, CNG tace zata fara zanga-zanga maras tsayawa daga ranar Alhamis mai zuwa, akan rashin tsaron da ke addabar arewacin Najeriya.
Kamar yadda kungiyar tace, za ta yi hakan ne don sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari irin halin da jihohin arewa 19 suke ciki. CNG tace, gwamnonin arewa sun gaza akan bai wa rayuka da dukiyoyin 'yan arewa cikakken tsaro, don haka tura ta kai bango.
Ba a harkar tsaro kadai gwamnonin suka kasa ba, har da karin kudi akan asalin kudin wutar lantarki.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng