Yanzu Yanzu: An yi zanga-zanga a Akure kan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya na ficewa daga jihar

Yanzu Yanzu: An yi zanga-zanga a Akure kan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya na ficewa daga jihar

- Mutane da dama a Ondo sun goyi bayan hukuncin Gwamna Rotimi Akeredolu na korar makiyaya daga jihar

- Domin nuna hakan, yan asalin jihar sun fito a ranar Alhamis, 21 ga watan Janairu, domin yin zanga-zanga kan ayyukan ta’assar da ake zargin makiyayan da aikatawa

- Mafi akasarin masu zanga-zangar sun yi ikirarin cewa makiyayan na da hannu a kashe-kashe da garkuwa da mutanen jihar

An gudanar da gagarumin zanga-zana a Akure, babbar birnin jihar Ondo a ranar Alhamis, 21 ga watan Janairu, inda direbobin motocin haya da mambobin kungiyar masu gadin dazzuka, manoma da yan kasuwa suka fito unguwanni.

Sun fito ne domin yin zanga-zangar goyon bayan umurnin da Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayar na neman makiyaya su bar yankin dazuka a jihar cikin kwanaki bakwai.

KU KARANTA KUMA: Ga abunda yan Igbo ke so daga Nigeria, Ohanaeze ta bayyana

Yanzu Yanzu: Ana zanga-zanga a Akure kan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya na ficewa daga jihar
Yanzu Yanzu: Ana zanga-zanga a Akure kan umurnin da Akeredolu ya baiwa makiyaya na ficewa daga jihar Hoto: The Nation
Source: UGC

Masu zanga-zangar sun dauki kwalayen sanarwa inda suka bukaci gwamnan na Ondo da kada ya janye umurninsa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shugaban kungiyar ma’aikatan sufuri na kasa, Kwamrad Jacob Adejo, ya ce yanzu direbobin motocin haya na cikin hatsari a jihar.

Adejo ya ce mambobin kungiyarsa na bukatar kariya yayinda makiyaya ke kai masu hari da kuma garkuwa da su.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun kama mambobin hatsabibiyar kungiyar nan ta yan Shilla su 3 a Yola

A gefe guda, kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, MACBAN, ta yabawa Fadar Shugaban Kasa saboda saka baki cikin batun umurnin da gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akerelodu ya bada na korar makiyaya daga dazukan da ke jiharsa.

Sakataren kungiyar na kasa, Usman Baba-Ngelzerma ya shaidawa The Punch a ranar Laraba cewa Fadar Shugaban Kasar ta fadi gaskiya a yayin da ta ce makiyayyan su cigaba da zamansu a jihar.

Baba-Ngelzerma ya ce kawo yanzu kungiyar ta makiyaya ba ta samu wani umurni a hukumance da ke neman su fice daga jihar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel