Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Muhammad Sanusi I rasuwa

Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Muhammad Sanusi I rasuwa

- Allah ya yi wa daya daga cikin ’ya’yan Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi I rasuwa

- Marigayiyar wacce aka fi sani da Fulanin Gandu ta amsa kiran mahaliccinta a yau Alhamis, 21 ga watan Janairu

- Ana sa ran yin jana’izarta a Kofar Kudu, Fadar Sarkin Kano da karfe 4:00

Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano na biyu, Muhammadu Sunusi I, Hajiya Hadiza Sanusi, rasuwa.

Hajiya Hadiza wacce aka fi sani da Fulanin Gandu, ta rasu ne a ranar Alhamis, 21 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Batanci ga Annabi: An tsaurara matakan tsaro yayinda kotu ke shirin yanke hukunci a Kano

Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Muhammad Sanusi I rasuwa
Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Muhammad Sanusi I rasuwa Hoto: @PremiumTimesng
Source: Twitter

Marigayiyar ta rasu ta bar 'ya'ya da dama daga ciki akwai Ambasada Ghali Umar da Sanusi Umar da sauransu.

Tashar Freeedom Radio ta ruwaito cewa daya daga cikin surukan marigayiyar, Sa’adatu Baba Ahmad ce ta sanar da batun mutuwar.

Za kuma ayi jana'izarta da misalin karfe 4:00 na yamma a Kofar Kudu ta fadar Sarkin Kano.

KU KARANTA KUMA: Hisbah a Kano ta sasanta ma'aurata 3,079 a shekarar 2020 kadai

A wani labari na daban, Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Jihar Kaduna, KAEDCO, a ranar Laraba, ya yanke wutar gidan marigayi Shehu Shagari, shugaban kasar Najeriya a jamhuriyya ta biyu, saboda bashin sama da miliyan 6.

Tsohon shugaban kasar ya rasu ranar 28 ga watan Disambar 2018, yana da shekaru 93.

Da ya ke tabbatar da lamarin yanke wutar a titin Sama, gidan tsohon shugaban da ke Sokoto, mai magana da yawun Kamfanin, Abdulaziz Abdullahi, ya ce ba a biya kudin wuta ba tun rasuwar Shagari.

A gefe guda, kotun daukaka kara dake zamanta a jihar Kano ta yi watsi da hukuncin daurin shekaru 10 da akayi wa Umar Farouq, matashin da ake zargi da kalaman batanci ga Annabi.

Bayan haka, kotun ta sake watsi da hukuncin da aka yiwa mawaki, Yahaya Aminu Sharif, inda ta ce a sake shari'ar daga farko, cewar rahoton BBC.

Shi ma Yahaya Aminu Sharrif ana zarginsa da kalaman batanci kan Annabi (SAW).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel